Manyan tonon sililin da sabon littafin Bisi Akande ya yi wa Obasanjo, Buhari, Atiku, da Dasuki
Littafin ‘My Participation’ da Bisi Akande ya rubuta a game da tarihin rayuwarsa, ya bayyana wasu abubuwa da mafi yawan mutane ba su sani ba
Legit.ng Hausa ta bi rahotanni da abubuwan da littafin ya kunsa, inda ta tattaro sababbin bayanai da tonon silili da dattijon ‘dan siyasar ya yi wa wasu
Daga cikin wadanda aka tabo a littafin ‘My Participation’, akwai Mai girma Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Haka zalika, wannan littafi ya taba irinsu Olusegun Obasanjo, Adebayo Adebanjo, Nuhu Ribadu, Olu Falae, Sambo Dasuki da abokinsa, Bola Tinubu
1. Tikitin Buhari-Tinubu a 2015
A littafin na sa, Bisi Akande ya bada labarin yadda Muhammadu Buhari ya yi alkawarin daukar Bola Tinubu a matsayin abokin takararsa a APC a zaben 2015.
Cif Akande yace a karshe hakan ba ta yiwu ba bayan wasu manyan ‘yan siyasar Arewa sun hurewa Buhari kunne, sai aka ba Tinubu zabi ya kawo ‘dan takararsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Atiku ya nemi kudi a hannun Bola Tinubu
Wani babban zargi da Bisi Akande ya yi a littafin na sa, shi ne cewa Atiku Abubakar ya yi ta neman kudi a hannun Tinubu a lokacin da yayi takara a AC a 2007.
Atiku Abubakar ya musanya wannan zargi, yace Cif Akande yana neman zaba karen farautar Tinubu.
3. ACN a zaben 2011
Da yake bayanin abubuwan da suka faru a zaben shugaban kasa na 2011, tsohon shugaban na APC yace Malam Nuhu Ribadu ya yi niyyar janyewa Muhammadu Buhari.
4. Sambo Dasuki ya nemi alfarma
A game da zaben 2011, Akande yace Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya roki shi da Bola Ahmed Tinubu dama jam’iyyar CAN ta bar wa Muhammadu Buhari takara.
5. Kutungwilar Obasanjo
Littafin ‘My Participation’ ya taba tsohon shugaba Olusegun Obasanjo inda aka tabo tarihin alakarsa da Bola Ige da yadda ya nakasa gwamnonin Yarbawa a 2023.
6. Olu Falae da Adebanjo
A cewar tsohon gwamnan na jihar Osun, Olu Falae da Adebayo Adebanjo sun halarci taron CONFAB da sunan manyan kasar Yarbawa ne saboda kudin da aka biya.
7. 1999: Olu Falae da APP
A karshe, Akande ya bayyana yadda jagororin jam’iyyar APP suka kawowa Cif Olu Falae cikas a lokacin da ya tsaya takarar shugaban kasa tare da Obasanjo a 1999.
Asali: Legit.ng