Ganduje ya yi bayanin rigimarsa da su Shekarau a APC, yace Jam'iyya za tayi masu sulhu
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana inda ake ciki a rikicin cikin gidan APC
- Abdullahi Umar Ganduje yace uwar jam’iyya ta tsoma bakinta domin a samu masalaha a jam’iyya
- Dr. Ganduje yake cewa dole a rika hakuri da juna a siyasa, kuma ya na sa ran a samu jituwa a APC
Kano – Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan sabaninsa da bangaren Malam Ibrahim Shekarau a rikicinsu na cikin gidan APC.
Da aka yi hira da shi a RFI Hausa, mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sam ba wani abin mamaki ba ne don an samu rashin jituwa a siyasa.
A cewar Dr. Abdullahi Ganduje, uwar jam’iyya ta na kan kokarin sasanta wannan rikicin cikin gidan.
“Ana nan ana sasantawa, kamar yadda ka sani, uwar jam’iyyar ta shiga. Kuma samun rabuwar kai a siyasa ba sabon abu ba ne, a daidaita ba sabon abu ba ne.”
“Saboda haka duka masu wannan, da dukkanmu ‘yan siyasa ne, mun san wani lokaci za a bata, wani lokacin kuma sai a shirya.” – Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Ganduje ya dade a wannan harkar
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021, Abdullahi Ganduje yace ba yau ya fara siyasa ba, gwamnan yace ya dade a wannan harka.
“Amma abin da muke cewa shi ne, wannan siyasa ba wai mun tsince ta a bakin titi ba ne. Mun shige ta ne fiye da shekara 40 da suka shige.”
“Kuma bugu da kari ma, ita mu ka karanta a jami’a, kuma ita mu ke yi. Saboda haka mun san siyasa harka ce ta hakuri.” – Gwamna Ganduje.
Hakarmu za ta cin ma ruwan sha - Ganduje
A jawabin na sa, gwamnan na Kano yace ba a yin abokin gaba da din-din a siyasa, sai dai ma abokin din-din-din saboda yadda mutane suke canza alkibla.
A karshe Abdullahi Ganduje yace ya na sa ran hakarsu za ta cin ma ruwa wajen sasanta ‘yan APC.
Rikicin cikin gidajen APC
A Kano abin ya yi kamari tsakanin Abdullahi Ganduje da tsaginsu Ibrahim Shekarau da Barau Jibrin. Rashin jituwar ta jawo aka samu shugabanni biyu a Kano.
Bangaren gwamnati su na tare da Abdullahi Abbas yayin da su Shekarau ke tare Ahmadu Danzago.
Asali: Legit.ng