Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

  • Ahmad Abba Dangata zai shiga takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC a zaben da za a shirya
  • Wannan matashi wanda yanzu yake karatun digiri a jami’ar ABU Zaria yace lokacin matasa ya yi
  • Dangata yace bai dace a bar wasu tsofa-tsofai su na darewa kujerun da aka warewa sa'o'insa ba

Kaduna – Ahmad Abba Dangata, matashi ne mai shekara 28, wanda ya ci burin ya rike mukamin shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa baki daya.

Malam Ahmad Abba Dangata wanda yanzu haka dalibi ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, zai yi takarar wannan kujera a zaben shugabannin APC.

A shekarar 1993 aka haifi Ahmad Abba Dangata a kauyen Kore, karamar hukumar Garki, jihar Jigawa.

Legit.ng ta samu labarin cewa Ahmad Abba Dangata zai yi amfani da damar da aka bada na barin kujerar shugaban matasan APC ga ‘yan kasa da shekara 35.

Kara karanta wannan

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

Karatun Ahmad Abba Dangata

Abusites.com tace matashin ‘dan siyasar ya fara yin karatun firamarensa ne a makarantar Kore Central Primary School, inda ya kammala a shekarar 2006.

Daga nan ya zarce makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Majia daga shekarar 2006 zuwa 2012. Sai ya wuce kwalejin ilmi da ke garin Gumel, Jigawa.

Ahmad Abba Dangata
Mai neman kujerar shugaban matasa na APC Hoto: Facebook Ahmad Abba Dangata
Asali: Facebook

Yanzu haka ya na karantar ilmin koyar da harshen Ingilishi a jami’ar ta Ahmadu Bello. Tun kafin ya gama makaranta, Dangata ya fara harin wannan kujera.

Meyasa ya ke neman kujera?

Ahmad Dangata ya na ganin lokaci ya yi da matashin gaske zai rike kujerar shugaban matasa, a madadin a rika barin wasu dattawa su na ci da gumin sa’o’insa.

Idan ya yi nasara a zaben da jam’iyyar APC za ta shirya a 2022, Dangata ya sha alwashin nemawa matasa dama a rika yi da su, sannan zai taimakawa sa'anin na sa.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Bugu da kari, Dangata yace zai fadakar da matasa a kan muhimmancin zaman lafiya da hadin-kai, tare da shigo da su cikin harkar siyasa, ba tare da bakar gaba ba.

Kadade Sulaiman ya zaburrar da matasa

Zaman Muhammad Kadade Suleiman shugaban matasa na PDP ya na cikin abin da ya burge Dangata, yace kowane matashi ya ji dadin ganin faruwar hakan.

Kwanakin baya mu ka kawo maku rahoto cewa Prince Muhammad Kadade Suleiman zai nemi mukamin shugaban matasa na jam'iyyar PDP na kasa baki daya.

A karshe dai matashin ‘dan siyasar mai shekara 25 rak a Duniya ne ya yi nasara a zaben da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng