A shekara kusan 70, magoya baya sun ce Tinubu bai tsufa da zama Shugaban kasa ba
- Kungiyar Tinubu Legacy Forum ba ta ganin Bola Ahmed Tinubu ya tsufa da yin takara a zaben 2023
- Magoya baya na cigaba da yin kira ga Bola Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC
- Shugabar 'Yan Edo Volunteers for Tinubu 2023 ta sha alwashin sayawa ‘dan siyasar fam din takara
Abuja - Wata kungiyar siyasa mai suna Tinubu Legacy Forum (TLC), ta ce jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, bai tsufa da shiga takarar shugaban kasa ba.
Duk da Bola Tinubu ya na daf da cika shekara 70 a Duniya, jaridar Daily Trust tace kungiyoyi irinsu TLC na cigaba da taya shi yakin neman shugaban kasa.
Shugaban tafiyar TLC na reshen jihar Abuja, Abdullahi Awwal Muhammad yace tsohon gwamnan bai tsufa ba domin kuwa tsofaffi sun yi shugabanci a Najeriya.
“Matasan kasar nan su goyi bayan burin jagoran jam’iyyar APC na kasa, ko da shi (Tinubu) bai take dokar ‘Not too young to run’ ba.
Dole matasanmu su koyi siyasa kafin su shiga takara. Tun a zamanin su Azikiwe, Tinubu yake koyon siyasa, a lokacin yana matashi.
“A halin yanzu, wadanda suka san jiya da yawa kawai ya kamata su rike mulki. Matasa su yi koyi da irinsu Tinubu da Atiku.” – Muhammad.
Tinubu zai gaji Buhari - Pa Okeowo
A daidai wannan lokaci aka ji jaridar Vanguard ta rahoto Raphael Aina Okeowo yana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai zama shugaban kasa a 2023.
Raphael Aina Okeowo yace Ubangiji ya nuna masa ‘dan siyasar zai gaji Muhammadu Buhari.
Mu zamu saya masa fam - Kungiya
Yayin da kiran da ake yi wa Tinubu ya yi takara ta ke kara karfi, ‘yan Edo Volunteers for Tinubu 2023 sun sha alwashin sayawa ‘dan siyasar fam din takara.
Shugabar tafiyar Edo Volunteers for Tinubu 2023, Adetutu Owolabi tace za ta fanshi fam din shiga takarar shugaban kasa da sunan gwanin na ta a zaben 2023.
“Domin kishin kasa, a madadin Edo Volunteers for Tinubu 2023,, zan yi farin cikin saya masa fam din APC idan lokacin ya zo, an bani dama.” – Owolabi.
Rikicin APC a Osun
An ji manyan APC a karkashin jagorancin Bisi Akande su na yunkurin yin sulhu tsakanin tsagin Gboyega Oyetola da Rauf Aregbesola APC kafin zaben 2022.
A 2022 za ayi zaben Gwamna a Jihar Osun, idan APC tayi wasa, PDP za tayi mata kafa. Wannan ya sa jiga-jigan jam'iyyar ke kokarin dinke barakar cikin gidan.
Asali: Legit.ng