Dattawa sun tsoma baki yayin da alakar Ministan Shugaba Buhari da Gwamnansa tayi tsami

Dattawa sun tsoma baki yayin da alakar Ministan Shugaba Buhari da Gwamnansa tayi tsami

  • An yi wani zama na musamman domin dinke barakar da ta bijirowa jam’iyyar APC a jihar Osun
  • Tsohon Gwamna Bisi Akande ya saurari kukan bangaren Adegboyega Oyetola da Rauf Aregbesola
  • Isaac Adewole, Hon. Lasun Yusuf, Ajibola Bashir, Benedict Alabi sun samu halartar zaman sulhun

Osun - Rigimar cikin gidan jam’iyyar APC a jihar Osun ya kara cabewa inda ba a ga maciji tsakanin gwamna Adegboyega Oyetola da Rauf Aregbesola.

Jaridar The Nation tace dattawan Osun a karkashin jagorancin Cif Bisi Akande, sun fara kokarin sasanta Rauf Aregbesola da magajinsa, Adegboyega Oyetola.

Nan da watanni bakwai za a gudanar da zaben gwamna a Osun, don haka aka fara kokarin dinke barakar cikin gidan da ya bijirowa jam’iyyar APC mai mulki.

Sola Akinwumi da wasu jagororin APC na jihar Osun sun yi zama a gidan Bisi Akande domin kawo karshen sabanin bangaren Gwamna da tsohon gwamna.

Kara karanta wannan

2023: Magoya bayan Osinbajo sun huro wuta, sun ce shi ya kamata ya karbi shugabanci

Yadda taron ya kasance

Wadanda suka halarci wannan zama sun hada da Gbadebo Ajao, Kunle Odeyemi, Titilaoye Ponnle, Prince Felix Awofisayo, Johnson Awofisayo, da Oye Oke.

Sai Isa Abimbola, Adeyemi Afolahan, Adepoju Odusola, Alhaji M.O Iyiola, Alhaji Sule Alao, Sooko Adewoyin Adeleke, Sola Ogunsanya, da Hon. Lasun Yusuf.

'Yan APC
Manyan APC a wajen kamfe Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Rahoton yace an ga Farfesa Razak Deremi, Farfesa Mojeed Alabi, da Gbadegesin Adedeji a taron.

An fara taron ne da karfe 11:15 na safe, an kuma tashi da karfe 1:30 na rana. Taron ya tabo muhimmancin hadin kai da hadarin a shiga zabe da rabuwar kai.

Kowane daga cikin bangarorin ya gabatar da korafinsa da zargin da ya ke yi wa ‘danuwansa gaban tsohon gwamna Bisi Akande, wanda ya taba rike APC.

Yusuf Lasun ya caccaki shugabannin APC

Kara karanta wannan

EFCC: Ma’aikacin banki ya tona yadda tsohon gwamna da SGG suka 'ci' N1.5bn a 2015

Tsohon mataimakin shugaban majalisa, Yusuf Lasun ya koka a kan yadda shugabannin APC na jihar Osun suka maida shi ba-kowa ba a lokacin Adams Oshiomhole.

Amma irinsu Sanata Ajibola Bashir sun maida martini, su ka wanke jagororin jam’iyya na reshen Osun, tare da godewa tsohon gwamna, Ogbeni Rauf Aregbesola.

Mataimakin gwamna, Benedict Alabi yace babu wani sabani tsakaninsu da mai gidansu, Aregbesola, yace jita-jitar mutane ce, amma su na tare da Ministan.

Olasupo Ladipo, Issa Ojewale, Prince Gboyega Famodun, Isaac Adewole, Oba Muhammed Babatunde da Omolaoye Akintola sun samu halartar wannan zama.

Yahaya Bello 2023

A makon nan kungiyar Global Alliance of Progressive Professionals ta nada Jagorori a fadin Najeriya domin yi wa gwamnan jihar Kofi yakin zama Shugaban kasa.

A wajen bikin rantsar da shugabannin tafiyar, Sanata Smart Adeyemi bayyana cewa yana goyon bayan Gwamna Yahaya Bello ya karbi mulkin Najeriya a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng