Atiku ya ba APC shawara ta dauki kwas a wajen Gwamonin PDP, ya caccaki duka Jihohin APC
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kaddamar da titin Gombe zuwa Maiduguri
- Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya gayyaci Atiku Abubakar zuwa Bauchi domin bude titin
- Atiku ya yabawa Gwamnan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki darasi da aikin jihohin PDP
Bauchi - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba jam’iyyar APC mai mulki shawarar ta yi koyi da jihohin da suke hannun jam’iyyar PDP.
Atiku Abubakar ya yi wannan kira ga jam’iyyar ta APC ne da yake kaddamar da titin Gombe zwa Maiduguri da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya kammala.
This Day ta rahoto Abubakar yana ba da shawarar da ta dauki darasi wajen gina abubuwan more rayuwa.
A cewar Alhaji Atiku Abubakar, wannan zai taimaka wajen rage matsalar rashin ayyukan yi, wanda suka yi sanadiyyar jawo rashin tsaron da ya addabi kasa.
Aikin titin Gombe-Maiduguri
Rahoton yace Gwamnatin Bala Mohammed ta gina wannan hanya mai tsawon kilomita 4.2, sannan ya sa mata sunan tsohon mataimakin shugaban kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku yace ya kamata mai girma gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya cigaba da irin wannan, ya rika kawo ayyukan da za su taba rayuwar mutanen Bauchi.
Jigon adawar kasar yace ayyukan more rayuwa su ne silar gyara tattalin arziki, da samar da abin yi, don haka ya nemi gwamnatin tarayya ta bi sahun jihohin PDP.
A cewar Atiku, jihohin da jam’iyyar PDP ta ke mulki sun yi zarra wajen gina abubuwan more rayuwa, idan aka kamanta da su sauran jihohin da ke hannun APC.
Atiku ya yabi Bala, ya soki APC
“Bari in yaba maka da ka rage rashin aikin yi a jiharka da Najeriya baki daya, domin rashin abin yi ne yake jawo matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.”
“Ina ma a ce gwamnatin tarayya za ta yi koyi da abin da jihohin PDP suke yi, domin duk jihar jam’iyyar PDP da ka je, za ka ga ana ayyuka.” – Atiku Abubakar.
“Ba zan iya tuna wata jihar APC da ta kaddamar da ayyuka ba. Saboda haka, gwamna ka kama hanyar dawo da PDP a jiha da kasar Najeriya baki daya.”
Osinbajo zai kai labari a 2023?
A ranar Alhamis ne aka ji wata Kungiya ta fito, ta na taya Yemi Osinbajo kamfe domin ya zama Shugaban Najeriya bayan wa'adin Muhammadu Buhari ya cika.
Kungiyar Progressive Consolidated Group ta roki Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya takara a zaben 2023, domin ya dace da mulki.
Asali: Legit.ng