Maganar Gwamna El-Rufa'i na rokon yan Najeriya kada su zabi PDP a 2023 ya bar baya da kura
- Gwamnan Kaduna ya roki yan Najeriya musamman mutanen jihar kada su kuskura su zabi jam'iyyar PDP a 2023
- Sai dai wannan magana ba tai wa yan Najeriya dadi ba, inda tuni wasu suka fara sukar gwamnan
- Mataimakin shugaban PDP a Mazabar Abia ta arewa ya maida wa El-Rufa'i martani mai ɗumi
Kaduna - Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya fara shan suka bayan ya roki yan Najeriya kada su zabi jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Vanguard tace El-Rufa'i ya yi ikirarin cewa matukar yan Najeriya suka yi kuskuren zaben PDP to zata maida hannun agogo baya.
Gwamnan, wanda ya yi wannan furucin a jiharsa Kaduna, ya kuma zargi sanatocin PDP biyu da suka shuɗe da gurgunta cigaban jihar Kaduna.
Bisa haka ne gwamnan ya roki al'ummar jihar Kaduna su guji PDP domin kada ta zo, "ta dawo da matsalolin jiya sabbi."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Elrufa'i ya fara shan suka
Da yake martani kan wannan magana, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na Abia ta arewa, Chief Amah Abraham, ya zargi gwamnan da kokarin take gaskiya.
Mista Abraham ya bayyana cewa APC ce ta maida Najeriya baya na tsawon shekara 50 daga inda PDP ta bar ƙasar a 2015 lokacin da tasha kaye a zaɓe.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda maimakon baiwa yan Najeriya hakuri bisa lalata tattalin arzikin kasa, har yanzu shugabannin APC na ɗora laifin akan PDP.
A martaninsa yace:
"Ya kamata El-Rufai ya bar yan Najeriya da kansu, su tantance tsakanin APC da PDP. A shekarar 2015 da APC ta ɗare kan mulki ana siyar da litar man fetur N89, amma yanzun ana saida lita N165."
"Kafin 2015 Najeriya ita ce ta biyu a kasashe masu tattalin arziki dake tasowa amma yau Najeriya karkashin APC ta zama ƙasa ta biyu mafi talauci a Duniya, abin kunya."
Komai ya yi tsada karkashin APC
Jigon PDP ya kuma kara da cewa komai ya ƙara tsada karkashin mulkin APC fiye da yadda PDP ta mika mata mulki a 2015.
"Iyali nawa ne zasu iya amfani da tukunyar Gas ta girki? Zubar da jinin mutane ya zama ruwan dare a Najeriya.."
"Ga dukkan alamun da suka bayyana Najeriya ta lalace karkashin APC. Cikin shekara 6 jam'iyyar APC ta maida Najeriya baya na tsawon shekara 50."
Martanin wasu yan Najeriya a shafin mu na Facebook
Jamila Bint Jibril tace:
"Allah ya zaɓa mana mafi Alkairy, amma gajerun mutane sun cika karambani."
Awwal Tasiu yace:
"Talakawa su zasu yi hukunci. Allah dai ya kaimu shekarar 2023."
Abdullahi Muazu yace:
"Mun ga halin kowa yanzun, dan haka a bar mu mu zaɓa mu darje."
A wani labarin kumaJam'iyyar APGA ta yi magana kan shirin sauya shekar Gwamnan Anambra, Obiano da Saludo zuwa APC
2023: Kada ku zabi jam'iyyar PDP, ku zabi wanda na yarda da shi, Gwamna El-Rufa'i ya roki yan Najeriya
Jam'iyyar APGA ta yi karin haske kan raɗe-radin da ake yaɗawa cewa gwamna Obiano da Soludo zasu koma APC.
Tun bayan kammala zaben gwamnan Anambra, jita-jita ta fara yawo cewa dama can sun sasanta da Buhari cewa zasu koma APC.
Asali: Legit.ng