Yakin neman zaben Tinubu ya shigo yankin Arewa, Matasa su na goyon bayan shi a Filato
- YEAT tana kira ga al’umma su dage wajen ganin Bola Tinubu ya dare kan kujerar Shugaban kasa
- Kungiyar magoya bayan ta na ganin tsohon gwamnan na Legas ya cancanta da mulkin Najeriya
- Nimjul Pennap yace Tinubu ya lakanin jagorancin al’umma da sha'anin siyasa, sannan bai da kabilanci
Plateau - Wata kungiyar matasa a jihar Filato ta sake jaddada kiranta ga Asiwaju Bola Tinubu cewa ya fito takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Kungiyar Youths Earnestly Ask for Tinubu, tace Asiwaju Bola Tinubu yana da duk abin da ake nema wajen ‘dan takarar kujerar shugaban kasar nan.
A ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, 2021, Vanguard ta rahoto kungiyar YEAT ta na wannan kira.
Shugaban kungiyar YEAT na kasa, Kwamred Nimjul Pennap ya zanta da ‘yan jaridar, inda ya yi kira ga al’ummar kasar nan su ba Tinubu goyon baya.
Pennap yace sun kafa tafiyar Youths Earnestly Ask for Tinubu ne da nufin su jawo hankalin tsohon gwamnan na Legas ya fito ya yi takara a zaben 2023.
“Tinubu yana da abin da ake bukata wajen cigaba da tafiya a kan turbar nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo.” - Nimjul Pennap.
“An kafa kungiyar (YEAT) ne domin a yada manufar takarar Tinubu a babban zabe mai zuwa.”
"Asiwaju Tinubu kwararren jagora na wanda muka yi imani cewa kasar nan tana bukatar sa. Ya cancanci wannan kujera (ta shugaban kasar Najeriya).”
“Mutum ne mai hada-kan al’umma tsakanin shiyyoyi, kabilu da kuma addinai, kuma zai iya hada-kan kasar nan. Ya yi wa jam’iyyar APC kokari sosai.”
An rahoto Pennap yana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai iya amfani da mutanen da ya sani a fadin Duniya wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.
YEAT tace ta lalubo kusan na APC a matsayin mai kishin-kasa, maras kabilanci, kuma sha kundum a siyasa da jagorancin al’umma wanda zai iya rike kasa.
Edo Volunteers for Tinubu 2023
Kafin yanzu kun ji cewa kungiyar Edo Volunteers for Tinubu 2023 ta na cikin wadanda suke tare da jagoran na APC, Bola Tinubu a zaben da za ayi a shekarar 2023.
Shugabar Edo Volunteers for Tinubu 2023, Owolabi Adetutu ta bayyana dalilinsu na goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu, tace zai dawo da akalar kasar nan a kan layi.
Asali: Legit.ng