Mai gida ya bar PDP da babatu, ya kori shugabanninta daga ofis a kan kudin haya

Mai gida ya bar PDP da babatu, ya kori shugabanninta daga ofis a kan kudin haya

  • Ana yawo da labari cewa kotu ta kori jam’iyyar PDP daga shagon da suka kama haya a jihar Legas
  • Mai magana da yawun bakin PDP a jihar Legas, Taofik Gani, yace bai san an yanke hukunci su tashi ba
  • Wanda ya ba PDP hayar shago a unguwar Ikeja-GRA yana kukan PDP ta hana shi kudin hayar shi

Lagos - A ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, 2021, aka rahoto cewa an kori shugabannin PDP na jihar Legas daga sakatariyar jam’iyya a dalilin kudin haya.

Jaridar Daily Trust tace an yi waje da shugabannin jam’iyyar adawar daga shagon da suke haya ne a dalilin an kai su kotu saboda sun gagara biyan kudin haya.

Kotu ta yanke hukunci ne bayan wanda ya mallaki wannan gini da yake kan titin Adekunle Fajuyi a unguwar Ikeja – GRA, ya kawo karar PDP a gaban Alkali.

Kara karanta wannan

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

‘Yan sanda da ma’aikatan kotu sun dura sakatariyar domin su kori shugabannin jam’iyyar PDP na Legas. Bayan kusan sa’a biyu da isarsu, suka fatattaki kowa.

Me jam'iyyar PDP take cewa a kan lamarin?

Vanguard tace mai magana da yawun jam’iyyar PDP a jihar Legas, Taofik Gani ya fitar da jawabi, inda yace ba zai iya cewa komai ba game da lamarin ba tukuna.

Iyorchia Ayu
Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu
Asali: UGC

Gani yace a lokacin da ake zargin abin ya auku, ba ya kasar, amma yace abin tir ne idan hakan ta faru. Kakakin na PDP ya tabbatar da cewa lallai ana bin su bashi.

Jami’in yace ya san da labarin akwai bashin da ake cewa ana bin jam’iyyar PDP, amma yace bai da labarin abin ya kai kotu don yin hakan na nufin an saba doka.

Kara karanta wannan

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

Jam'iyyar PDP ta fito, tayi Allah-wadai.

“’Yan jarida da sauran jama’a suna ta kira na, suna nuna damuwarsu, da kuma tabbatar da cewa ko da gaske kotu ta karbe hedikwatar jama’iyya a Legas.”
“Da gan-gan aka shirya wannan domin a kunyata PDP, a kawowa jam’iyyar adawa matsala.” - Gani.

Rikicin APC a jihohi

A Jihohin Kano da Legas, an kama hanyar shawo kan rigimar da ta bullowa Jam’iyyar APC. Tsagin Sanata Ibrahim Shekarau sun bada sharadin yi sulhu.

Jiga-jigan APC a irinsu Kwara da Imo sun ki yarda Jam’iyya tayi masu sulhu da Gwamnoni. Amma a Legas, 'yan taware sun zauna gaban kwamitin NRC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng