2023: Masu neman takarar gwamna 7 daga APC da PDP na shirin sauya sheka zuwa APGA a wata jihar kudu maso gabas
- Nasarar da jam'iyyar APGA ta samu a zaben gwamnan jihar Anambra ya kara mata farin jini a yankin kudu masu gabashin kasar
- A yanzu haka wasu masu neman takarar gwamna 7 na APC da PDP na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar a jihar Imo gabannin zaben 2023
- A ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba ne dai dan takarar jam'iyyar ta APGA, Charles Soludo ya lashe zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra
Imo - Rahotanni sun kawo cewa wasu masu neman takarar gwamna su bakwai sun nuna aniyarsu ta komawa jam’iyyar All Progressive Grand Alliance, APGA, reshen jihar Imo domin kwato mulki daga hannun APC a 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yunkurin wadannan yan siyasa baya rasa nasaba da nasarar da jam'iyyar APGA ta yi a zaben gwamnan Anambra wanda aka yi a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
A zaben na Anambra, dan takarar APGA, Charles Soludo ne ya lashe zaben inda ya lallasa yan takarar manyan jam'iyyun adawa na PDP da APC.
Jaridar ta kuma rahoto cewa masu uku daga cikin masu neman takarar da ke shirin sauya sheka sun fito ne daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Sannan sauran masu neman takarar hudu da suka nuna aniyar sauya shekar sun fito ne daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasar.
Sai dai kuma shugaban APGA a jihar Imo, John Iwuala, bai ambaci sunayensu ba amma ya ce yana ta samun sakonnin taya murna tun bayan nasarar jam'iyyar a Anambra.
Bincike ya nuna cewa mafi akasarin masu neman takarar gwamnan daga APC da PDP sun bukaci magoya bayansu da su gaggauta yin rijista a APGA gabannin yakin neman zabe na shekara mai zuwa.
Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1
A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya yiwa wata mata mai suna Misis Eunice Ngozi Onuegbusi kyautar zunzurutun kudi har naira miliyan 1.
Misis Onuegbusi, mutuniyar Ukwulu (kauyen Magu) Ward 1, rumfar zabe ta 04 a karamar hukumar Dunukofia da ke jihar, ta ki amsar N5,000 daga wakilin wata jam’iyya a yayin zaben gwamnan Anambra da aka kammala.
A cikin wani bidiyo da ya karade yanar gizo, an gano yadda Madam Eunice ta ki amsar N5,000 daga wakilin wata jam’iyya a rumfar zabenta a lokacin zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng