Charles Soludo: Muhimman abubuwa 10 da ya dace ku sani game da zababben gwamnan Anambra
- Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APGA, Charles Soludo, ya ci nasara a kan manyan abokan takarar sa har a kananun hukumomin su
- Soludo ya ci nasara a kan Andy Uba da Valentine Ozigbo a karamar hukumar Aguata, wadanda su ne manyan ‘yan hamayyarsa
- Cikin gundumomi 20 da ke karamar hukumar, Soludo ne ya lashe Isuofia, Nkpologwu, Igbo-Ukwu I da II, Ekwulobia II, Umuchu I da II, da sauran su
Anambra - An bayyana Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Baya ga zama gwamnan babban bankin Najeriya, akwai wasu abubuwa da yawa da ya kamata ka sani akan wanda ya gaji Willie Obiano a gwamnan jihar Anambra.
Anan akwai abubuwa 10 da ba lallai ka sani ba akan wanda ya lashe zaben jihar Anambra:
1. Ya kammala karatun sa da digiri mai daraja ta daya a fannin tattali.
Ya yi karatunsa a fannin tattalin arziki a jami’ar Nsukka kuma ya gama da digiri mai daraja ta daya a shekarar 1984.
2. Shi ne dalibin da ya fi ko wanne dalibi hazaka a shekarar da ya gama digirin sa na farko da na biyu
A digirin sa na farko, tsohon gwamnan bankin ya lashe manyan kyautuka na zama dalibi mafi hazaka. Soludo ya gama digirin digirgir a 1989 a jami’ar Nsukka. Kuma har kyautukan shugaban jami’ar na musamman sai da ya lashe su.
3. Ya koyar a jami’a na tsawon shekaru 15
Duk da kowa ya san dan siyasa ne, amma sai da ya yi shekaru 15 ya na koyarwa a jami’ar Nsukka, daga watan Fabrairun 1988 zuwa Yulin 2003.
4. Ya wallafa kasidai fiye da 82 a fannin ilimi
Soludo ya yi rubuce-rubuce na littafan ilimi fiye da 82, sai kuma takardun da ya gabatar gaban jama’a fiye da 220. Ya kuma tace wasu littafan.
5. Ya yi aiki a ma’aikatun kudi da ke kasashen ketare
Soludo ya yi aiki da ma’aikatun kudi na kasashen ketare kamar International Monetary Fund, IMF, World Bank, Washington DC da African Development Bank, AfDB.
6. Shugabanni 2 na kasa daga jam’iyyu mabanbanta sun ba shi mukamai (PDP da APC)
Olusegun Obasanjo daga jam’iyyar PDP ya taba nada shi mukamin mai bayar da shawarwari a fannin tattali daga Yulin 2003 zuwa Mayun 2004.
Sannan a 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi cikin kungiyar ma su bayar da shawarwari a fannin tattali.
7. Ba wannan ne karon Soludo na farko da ya yi takarar gwamna ba
A shekarar 2010 ya nemi takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP inda dan takarar APGA, Peter Obi ya maka shi da kasa.
Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi a Gombe
8. Kwararren dan wasan kwallon kafa ne
A wata tattaunawa da The Guardian ta yi da shi a 2016, Soludo ya bayyana cewa ya iya kwallo amma a boye yake yi.
Ya ce a lokacin su ba a daukar mutum da muhimmanci idan ya na kwallo ko kuma ya na waka.
9. Daya daga cikin yaran Soludo akwai mawaki
Soludo ya bayyana dalilan da su ka sa ya bar dan shi ya zama mawaki. Ya kuma nuna cewa dari bisa dari ya na goyon bayan wakar da dan sa Ozonna ya ke yi.
10. Shi ne mijin Nonyelum Frances Soludo
Duk da Soludo fitaccen mutum ne, matarsa Nonyelum Frances Soludo ba ta bayyana kan ta a idon duniya ba. Akwai mutane da dama da har yanzu ba su san ta ba.
Asali: Legit.ng