Zaben Anambra: Babu abinci, dan sanda ya koka kan yunwar da ta addabe shi
- A daidai lokacin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra, wani jami'in dan sanda ya koka kan yunwar da ta addabe shi
- Jami'in wanda ke tallafawa jami'an zabe wajen gudanar da aikinsu, ya yi korafin cewa ba a yi masu tanadin abincin da za su ci ba
- Kimanin jami'an yan sanda sama da 30,000 aka tura jihar domin zaben wanda ke gudana a a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba
Anambra - A yanzu haka ana nan ana ci gaba da gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Yayin da zaben ke gudana, wani jami'in dan sanda da ke aiki a rumfar zabe ta PU8, Abagana ward 2, karamar hukumar Njikoka, ya koka a kan yunwar da ta addabe shi.
Jami'in tsaron wanda aka boye sunansa ya bayyana cewa babu wani tanadi da aka yi masu na abinci, Jaridar Daily Trust ta rahoto.
An kuma tattaro cewa dan sandan shine ya taimakawa jami'an zabe a lokacin da ake tantancewa da gudanar da zaben.
Kimanin jami'an yan sanda sama da 30,000 aka tura jihar domin zaben wanda ke gudana a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
A wani labarin, mun kawo a baya cewa an fara gudanar da zabe a yawancin yankunan Awka, babbar birnin jihar Anambra inda aka girke jami'an tsaro da yawa a yankin.
Jami'an tsaro sun kuma fara binciken mutane da ababen hawan da ke ketarawa a yawancin yankunan babbar birnin jihar, inda suka bukaci su nuna katin zabensu kafin su basu damar wucewa.
Wakilin Legit.ng wanda ke yawon karade birnin ya lura cewa har yanzu mutane basu fito ba sosai domin yin zaben.
A wata rumfar zabe a Okpuno Awka, mutanen da aka gani basu kai guda dari ba a rumfar da ke da sama da mutane dubu masu rijista.
Asali: Legit.ng