An gano yadda Wike, Tambuwal da Gwamnoni suka raba mukaman PDP a tsakaninsu
- A makon da ya gabata ne jam’iyyar hamayya ta PDP ta shirya babban zaben shugabannin ta na kasa.
- Gwamnonin Benuwai, Ribas, Adamawa da Bauchi sun tashi da kaso mai tsoka a zaben da aka yi.
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya hada-kai da gwamnonin PDP, ya samu kujera.
Abuja - Daily Trust ta samu bayanai a game da yadda gwamnonin jam’iyyar PDP suka raba mukaman shugabanni a majalisar gudanarwa na NWC.
Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun nuna karfinsu a zaben shugabanni na kasa da aka yi, duk da maslaha aka bi wajen fito da sababbin shugabannin.
Gwamnonin da suka taka rawar gani sosai a zaben sun hada da Ahmadu Fintiri, Bala Muhammed, Samuel Ortom, Seyi Makinde da Aminu Tambuwal.
Haka zalika akwai gwamna Nyesom Wike wanda shi ne ya dage a kan tsige Uche Secondus.
Yadda zaben mukaman NWC ya kasance
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya taimaka wajen zaman Iyorchia Ayu shugaban jam’iyya. Sanata Ayu da Ortom sun fito ne daga jiha daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An gano Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ne ya yi ruwa, ya yi tsaki wajen ganin Sanata Samuel Ayanwu ya zama sakataren jam’iyyar PDP na kasa.
Haka zalika Umar Bature ya zama sakataren gudanarwa ne da goyon-bayan Aminu Waziri Tambuwal. Gwamnan Sokoto ne shugaban gwamnonin PDP.
Amb. Umar Iliya Damagum ya iya doke Hajiya Inna Ciroma ne da taimakon gwamnonin Adamawa da Bauchi; Umaru Fintiri da Bala Mohammed.
Ya ta kaya da Namadi Sambo da Bukola Saraki?
Muhammed Kadade Suleiman wanda ya zama shugaban matasan PDP yana tare da Ahmad Makarfi, ya doke ‘dan takarar Namadi Sambo, Usman El-Kudan.
A wani kaulin ana cewa El-Kudan wanda ya sha kashi, ya janyewa Kadade Sulaiman. Wata majiyar tace Sanata Makarfi ne ke rike da jam’iyya a Kaduna.
Shi kuwa Bukola Saraki ya san yadda ya yi ya kawo Kamal Adeyemi Ajibade a matsayin mai ba jam’iyya shawara kan harkar shari’a, ta hanyar yin maslaha.
Yadda Gwamnoni suka dama, aka sha
A wani rahoton, kun ji ‘Yan takarar da Gwamnonin jam'iyyar PDP suka marawa baya ne suka yi nasara zaben PDP, inda aka gwabza kan mukaman NWC.
Manyan PDP irinsu tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Sule Lamido da ba su rike da wata kujera yanzu a Gwamnati ba su samu komai ba.
Asali: Legit.ng