2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnoni ba su da hurumin yanke shawara kan yankin da zai samar da shugaban kasa na gaba
  • Tsohon gwamnan Kanon ya sanar da cewa, jam'iyyun siyasa ne kadai za su iya zama su tantance tare da bayyana wanda suke so ya tsaya takararsu
  • Kwankwaso ya ce babu wanda ya isa ya zauna a Legas ko wata jihar arewa ya yanke wanda zai zama shugaban kasa, fata dai a samu wanda zai yi abinda ake so

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Juma'a ya ce bai yanke shawarar fitowa takarar shugabancin kasa a 2023 ba.

Daily Trust, Kwankwaso ya kara da cewa, gwamnonin jihohi ba za su iya zama a Legas ko wani wuri a arewa ba su yanke shawarar wanne yanki ne zai samar da shugaban kasa na gaba ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso
2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce wannan hukuncin jam'iyyun siyasa ne kadai za su iya yanke wa bayan duba duk abubuwan da suka dace, ya kara da cewa abinda ya fi dacewa kuwa shi ne samun mutumin da ya fi dacewa da shugabancin.

Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi da gidan talabijin na AriseTV, inda ya caccaki mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana cewa sam bai gamsu da tsarin mulkin Ganduje ba.

Ya caccaki tsarin jihar na cin bashi mai tarin yawa inda ya ce a halin yanzu jihar Kano na dawainiya da bashin da ya kai N187 biliyan wanda kuma bai dace.

A yayin da aka tambaye shi ko zai fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023, ya ce, "Ban riga na yanke wannan shawarar ba."

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Naɗa ɗan shekara 66 shugaban kwamitin soshiyal midiya ya janyo cece-kuce

Sanata Kwankwaso ya yi magana a kan sake sauya-sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC

A wani labari na daban, tssohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a game da rade-radin da ake yi na cewa yana shirin barin PDP.

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana nan a jam’iyyar PDP. Kwankwaso ya yi karin-haske da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise.

Shugaban darikar siyasar Kwankwasiyyan ya yi wannan martani ne yayin da aka jefa masa tambaya kai-tsaye da ake hira da shi a game da makomarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng