Rashin tabbas a PDP, kila a fasa gudanar da zabukan sababbin shugabannin jam’iyya
- Prince Uche Secondus ya shigar da karar da zai iya zama cikas a jam’iyyar PDP
- Shugaban jam’iyyar da aka dakatar yana kalubalantar sauke shi da aka yi a kotu
- Idan Secondus ya yi nasara, watakila dole jam’iyya ta dakatar da shirin yin zabe
Abuja - Akwai kalubale a jam’iyyar PDP a game da zaben shugabanni na kasa da za ayi ranar Asabar, saboda yiwuwar kotu ta dakatar da shirya gangamin.
Hakan ya bayu ne ga kafewar Prince Uche Secondus wanda ya ki janye karar da ya shigar a kotu, yana kalubalantar sauke shi da aka yi kafin cikar wa’adinsa.
Sakataren shirya wannan zabe na kasa, gwamnan Oyo Seyi Makinde yace zaben na nan ranar Asabar.
The Nation tace gwamonin jam’iyyar PDP sun tattaro lauyoyi domin su takawa Uche Secondus a babban kotun daukaka kara da ke garin Fatakwal, jihar Ribas.
Lauyoyin za su kawo mafita idan har kotu ta dakatar da shirin zaben, sannan za a nemi a ji akwai kotun da za ta iya tsaida zaben da yiwuwar a tafi har kotun koli.
Rahoton yace masu kada kuri’a a zabukan da za a gudanar sun rasa inda za su sa gaba a halin da ake ciki. Babu tabbacin gangamin zai kankama a ranar Asabar.
Gwamnoni sun koka a kan zaben shugabanni
Haka zalika gwamnonin jihohi suna kukan cewa ba a tafiya da su. Ahmadu Fintiri, Seyi Makinde da Douye Diri ne kadai suka san abin da yake wakana a PDP.
Jaridar Punch tace a yau Talata, 26 ga watan Oktoba, 2021 ne za a saurari karar da Uche Secondus ya shigar, wanda ka iya jawo a daga sabon zaben gaba daya.
Lauyan da ke kare tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP, Tayo Oyetibo (SAN), ya shaidawa manema labarai cewa babu maganar janye shari’a a kotun daukaka kara.
A daidai wannan lokaci kuma Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan yace a an gama neman wurin da za a gudanar da zaben shugabannin.
Za a sake komawa kotu da Kalu
A yau ne aka fahimci cewa watakila tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu zai fuskanci sabuwar shari’a a kan zargin wawurar wasu Naira Biliyan 7.1.
Kotu ta taba daure Kalu na tsawon shekaru 12 a gidan maza, bayan wani lokaci sai ya fito. Hukumar EFCC ta nemi Alkali ya sake daure Sanatan na Abia.
Asali: Legit.ng