An hurowa Buni wuta ya hukunta Shekarau, Aregbesola, ya koyawa manyan APC hankali

An hurowa Buni wuta ya hukunta Shekarau, Aregbesola, ya koyawa manyan APC hankali

  • Gwamnoni suna so majalisar Mai Mala Buni ta hukunta wadanda suka bangare
  • Akwai jihohin da aka samu shugabanni fiye da daya a zaben shugabanni na APC
  • Shekarau, Amosun, Okorocha, da Aregbesola suna fuskantar matsala a jam’iyya

Abuja - Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, yana fusakantar matsin lamba a game da zaben shugabanni da aka gudanar.

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust tace an taso Mai Mala Buni a gaba, ana so ya hukunta wasu daga cikin ‘yan jam’iyya da suka shirya zaben taware a APC.

A dalilin rikicin da ake fama da shi tsakanin wasu jagororin APC na kasa da gwamnonin jihohinsu, ‘yan taware sun ja daga a zaben shugabannin jihohi.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Wani daga cikin gwamnonin jihar da aka samu shugabanni fiye da daya, ya taso uwar jam’iyya a gaba, yana so a hukunta wadanda suka raba kan ‘yan jam’iyya.

Jihohin da babu zaman lafiya a APC

An samu irin wannan rigima a Kano, Legas, Ogun, Kwara, Osun, Filato, Neja, Akwa Ibom, da Enugu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mala Buni
Wasu shugabannin APC na kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daga cikin wadanda ke kan gaba wajen goyon bayan wadanda ake ganin ‘yan taware akwai Ibrahim Shekarau (Kano), da kuma Ibikunle Amosun (Ogun).

Har ila yau akwai irinsu Rauf Aregbesola (Osun), Sanata Rochas Okorocha (Imo), Akinwunmi Ambode (Lagos), da Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom)

A jihar Osun, bangaren Rauf Aregbesola sun kai kara kotu a game da zaben da aka shirya. Hakan ya saba wa umarnin da shugabannin jam’iyyar APC suka yi.

Wata majiya tace gwamnoni na so a hukunta masu ja da su domin a koya wa wasu hankali yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shugabanni na kasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

Sakataren APC, John James Akpan Udo-Edehe yace ba za su yarda a raba kan jam’iyya ba. Amma Mala Buni ya musanya rade-radin cewa an huro masa wuta.

APC za ta lashe zaben Anambra

A ranar Laraba aka ji ‘Dan takarar Gwamnan APC a jihar Anambra, Sanata Ifeanyi Uba yana cewa Matar Gwamnan Anambra za ta bar APGA, ta shigo jirgin APC.

Hakan na zuwa ne bayan an ji Mataimakin Gwamnan Anambra, Dr. Nkem Okeke ya fice daga jam'iyyar APGA makonni kadan kafin a yi zaben sabon gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng