2023: Osinbajo da Tinubu za su yi zaman farko a game da shirye-shiryen zaben shugaban kasa
- Kusoshin APC sun fara tunanin yadda za su fito da ‘Dan takarar shugaban kasa
- Jagoran APC, Bola Tinubu zai yi zama na musamman da Farfesa Yemi Osinbajo
- Ana tunanin jam’iyyar mai mulki za ta guji samun rigima a zaben fitar da gwani
Abuja - Jaridar Punch tace akwai alamun cewa jam’iyyar APC za ta fitar da ‘dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ne ta hanyar yin maslaha.
Wani babban jigo a jam’iyyar APC, ya shaida wa jaridar cewa kusoshin APC sun fara tattauna wa a tsakaninsu a kan yadda za a bullo wa zabe mai zuwa.
Rahoton yace jagororin jam’iyyar suna ganin idan masu neman takarar shugaban kasa da yawa suka fito, mummunan rigima za ta iya barke wa a APC.
Majiyar tace wannan ya sa ake kokarin guje wa rudani a zaben fitar da gwani, ta hanyar tsaida ‘dan takarar da kowa zai yi masa mubaya’a a zaben 2023.
Yemi Osinbajo zai hadu da Tinubu
An samu labari cewa jagoran APC a Kudu maso yamma, Asiwaju Bola Tinubu zai zauna da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a kan batun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ashiwaju Bola Ahmed Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo za su zauna kwanan nan domin su tattauna a kan abubuwan da suka shafi zaben 2023.”
“Shugabannin jam’iyya na kokarin tsaida ‘dan takaara ta hanyar maslaha, a fito da wanda fadar shugaban kasa za ta sa wa albarka.” – wata majiyar.
Idan hakan ta tabbata, babu mamaki wannan ne karo na farko Farfesa Yemi Osinbajo zai zauna da tsohon mai gidansa tun bayan dawowarsa daga kasar waje.
Wani wanda ya san wadannan mutane biyu yace duk da Yemi Osinbajo bai kai wa Tinubu ziyara da yake kwance ba, ‘yan siyasar suna tattauna wa a kai-a kai.
Hakan ya kara tabbatar da cewa babu wani sabani tsakanin Bola Tinubu da tsohon kwamishinan na shi.
Femi Fani-Kayode ya karbi katin 'dan jam'iyya
Kwanan nan aka ji cewa Cif Femi Fani-Kayode ya karbi katinsa na zama cikakken ‘dan jam’iyyar APC. Kwanaki Fani-Kayode ya sauya-sheka daga jam'iyyar PDP.
FFK yace babu da-na-sani a kan sauya-shekarsa daga jam’iyyar hamayya zuwa APC. Tsohon Ministan ya yi alkawarin taimaka wa wajen rusa PDP a Najeriya.
Asali: Legit.ng