APC da PDP ba za su taba sauyawa ba: Jega ya bayyana matsalolin APC da PDP
- Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega ya sake bayyana wasu matsalolin jam'iyyun APC da PDP
- A cewarsa, jam'iyyun ba za su taba canzawa ba, kuma ba za su iya kawo wani ci gaba ba a yanzu
- Ya kuma ce, sabuwar jam'iyyar da yake aiki don kafawa za ta yi aiki tukuru don ganin ta kawo mafita ga 'yan Najeriya
Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi zargin cewa jakunkunan kudi da ubannin gida sun mamaye manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya kuma rashin dimokradiyyar cikin gida a cikin jam’iyyun na iya haifar musu da rudani.
Jam'iyyar PDP da ta APC sune manyan jam'iyyun Najeriya, kamar yadda da yawa kowa ya sani.
Jega, wanda ya yi magana ne a wani shirin talabijin a Legas, jiya, ya ce ba zai yiwu APC da PDP su canza su yi abin da ya dace ba kamar yadda ya bayyana a cikin fitinar taron gangamin da suka gudanar kwanan nan, Daily Sun ta ruwaito.
Ya koka da cewa bayan shekaru 22 na mulkin dimokradiyya, har yanzu Najeriya ta gagara kawar da kanta daga mummunan tasirin mutanen da ke ganin jam’iyyun siyasa a matsayin ababen hawa na musamman don cin zabe da gina kansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma ce lokaci har yanzu bai yi ba da za a bukaci jam'iyyun siyasa su gudanar da zaben fitar da gwani kai tsaye.
Jega ya ce zai zama aiki babba ga sabuwar jam'iyyar da suke kafawa don finke APC da PDP, amma ba abu ne da ba zai yiwu ba bisa jajircewar mutanen da abin ya shafa.
APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu
Tshon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.
A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.
Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.
Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas
A bangare guda, Rikicin da ya barke a cikin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya dauki wani sabon salo na daban.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa bangaren da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, ya kaddamar da babban jami’in gudanarwar sa.
A cewar rahoton, an yi bikin ne a Freedom House, sakatariyar yakin neman zaben da Sanata Abe ya kafa a GRA ta Fatakwal.
Asali: Legit.ng