KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya

Jam'iyyar All Progressives Congress APC na gudanar da taron gangamin shugabanninta na jihohi a fadin tarayya a yau Asabar, 16 ga watan Oktoba, 2021.

Yayinda wasu jihohi sun riga sun kammala zabukansu kuma sun yi ittifaki kan shugabanninsu, wasu jihohi na kada kuri'a.

Legit na kawo muku labaran abubuwan dake faruwa da duminsu.

Alhaji Haliru Zakari Jikantoro yayi daram dam kan kujerar shugaban APC a jihar Neja

An tabbatar da Alhaji Haliru Zakari ne a taron gangamin da aka gudanar a jihar Neja.

Daga cikin wadanda ke hallare akwai gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, mataimakinsa; da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar da jigogin jam'iyya

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya Hoto: Mary Berje Noel
Source: Facebook

An yi ittifaki Jekada ya cigaba da zama Shugaban APC a Kaduna

An tabbatar da Emmanuel Jekada ne a taron gangamin da aka gudanar a dakin Yar'adua dake Murtala Mohammed Square.

Shugaban kwamitin zaben, Abubakar Moddibo, ya sanar da cewa dukkan wadanda ke rikon kwarya ne aka tabbatar.

Daga cikin wadanda ke hallare akwai gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, mataimakiyarsa Hadia Balarabe; Kakakin majalisar jihar, Yusuf Ibrahim Zailani, dss.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Omotoso ya zama sabon shugaban APC na jihar Ekiti

An tabbatar da Omotoso ne a taron gangamin da aka gudanar da Mini Pavilion dake Ado Ekiti.

Shugaban kwamitin zaben, Yusuf Galambi, ya sanar da cewa dukkan wadanda ke rikon kwarya ne aka tabbatar.

Saboda haka ba'a gudanar da wani zabe ba.

Omeni Sobo ya zama sabon shugaban APC a jihar Delta

An zabi Don. Omeni Sobotie a matsayin sabon Shugaban jam'iyyar APC a jihar Delta.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
Source: Facebook

Amaechi a layi yana shirin kada kuri'arsa a Rivers

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya shiga layin domin kada kuri'arsa na jihar ta Rivers.

Amaechi wanda tsohon gwamnan Rivers ne jagoran APC a jihar.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya Hoto: Anayo Onukwugha
Source: Facebook

An kammala na jihar Borno, dukkan shugabannin zasuyi tazarce

Mambobin jam'iyyar APC a jihar Borno sun yi ittifakin cewa dukkan shugabannin jam'iyyar na yanzu karkashin jagorancin, Ali Dalori, su cigaba da gashi kawai.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan, ya bada shawaran hakan kuma mataimakinsa Abdullahi Askira, ya bada goyon baya.

Online view pixel