KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar APC ke gudana a fadin tarayya
Alhaji Haliru Zakari Jikantoro yayi daram dam kan kujerar shugaban APC a jihar Neja
An tabbatar da Alhaji Haliru Zakari ne a taron gangamin da aka gudanar a jihar Neja.
Daga cikin wadanda ke hallare akwai gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, mataimakinsa; da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar da jigogin jam'iyya

Source: Facebook
An yi ittifaki Jekada ya cigaba da zama Shugaban APC a Kaduna
An tabbatar da Emmanuel Jekada ne a taron gangamin da aka gudanar a dakin Yar'adua dake Murtala Mohammed Square.
Shugaban kwamitin zaben, Abubakar Moddibo, ya sanar da cewa dukkan wadanda ke rikon kwarya ne aka tabbatar.
Daga cikin wadanda ke hallare akwai gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, mataimakiyarsa Hadia Balarabe; Kakakin majalisar jihar, Yusuf Ibrahim Zailani, dss.

Source: Facebook

Source: Facebook
Omotoso ya zama sabon shugaban APC na jihar Ekiti
An tabbatar da Omotoso ne a taron gangamin da aka gudanar da Mini Pavilion dake Ado Ekiti.
Shugaban kwamitin zaben, Yusuf Galambi, ya sanar da cewa dukkan wadanda ke rikon kwarya ne aka tabbatar.
Saboda haka ba'a gudanar da wani zabe ba.
Omeni Sobo ya zama sabon shugaban APC a jihar Delta
An zabi Don. Omeni Sobotie a matsayin sabon Shugaban jam'iyyar APC a jihar Delta.

Source: Facebook
Amaechi a layi yana shirin kada kuri'arsa a Rivers
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya shiga layin domin kada kuri'arsa na jihar ta Rivers.
Amaechi wanda tsohon gwamnan Rivers ne jagoran APC a jihar.

Source: Facebook
An kammala na jihar Borno, dukkan shugabannin zasuyi tazarce
Mambobin jam'iyyar APC a jihar Borno sun yi ittifakin cewa dukkan shugabannin jam'iyyar na yanzu karkashin jagorancin, Ali Dalori, su cigaba da gashi kawai.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan, ya bada shawaran hakan kuma mataimakinsa Abdullahi Askira, ya bada goyon baya.