Sanatan APC ya ware Naira miliyan miliyoyi, zai biya kudin karatun yara 600 a garuruwan Legas
- Sanata Tokunbo Abiru zai share wa dalibai marasa karfi 600 hawaye a jihar Legas
- Tokunbo Abiru ya dauki nauyin biyawa mutune rututu kudin makaranta a yankinsa
- ‘Dan majalisar dattawan yace ya yi alkawari zai bunkasa harkar ilmi a mazabarsa
Abuja - Sanata Tokunbo Abiru mai wakiltar mazabar Legas ta gabas a majalisar dattawa na kasa, zai raba kyautar Naira miliyan 30 ga mutanen yankinsa.
Jaridar Daily Trust tace Sanata Tokunbo Abiru ta fitar da wadannan makudan kudin domin mutanen da yake wakilta a majalisa su samu damar karatu.
An shirya wani biki a babbar makarantar koyon aiki na jihar Legas (Lagos Polytechnic), inda Tokunbo Abiru ya bayyana wannan shiri da ya zo da shi.
‘Yan majalisar dokokin jihar Legas da wani tsohon mataimakain gwamna da shugabannin jami’a da sarakunan gargajiya na yankin sun halarci wannan bikin.
‘Dan majalisar yace an yi amfani da cancanta wajen zakulo wadanda za su amfana da wannan tsari.
Abin da ya sa mu ka kawo wannan shiri - Abiru
“Manufar wannan shiri ita ce a dage a kan neman ilmin gaba da sakandare mai nagarta, ta hanyar karfafa wa masu basirar da ke da kalubalen biyan kudin makarantu domin su samu ilmi.”
“A karon farko da za a aiwatar da wannan shiri, an zabi dalibai 600 daga mazabu 98 a kananan hukumomi 16 na yankin gabashin jihar Legas.” – Sanata Tokunbo Abiru.
Majalisar da ke kula da asusun tallafin dalibai a jihar Legas ta tantace duk daliban da aka zakulo.
Sanatan yace mafi kankantan abin da shugabanni za su iya yi shi ne su cika wa talakawa burin da suke da shi a rayuwa, muddin sun fito ne daga mazabarsu.
‘Dan majalisar yace daga cikin yarjejeniyar da ya dauka da mutanen Legas ta gabas shi ne zai dage wajen karfafa wa matasa, shiyasa ya zo da wannan shirin.
A watan Nuwamba, Sanata Abiru zai hada-kai da wani kamfani domin a tallafa wa kananan ‘yan kasuwa.
Asali: Legit.ng