Shugabancin 2023: Jerin manyan jiga-jigan PDP da ke son a bude tikitin jam’iyyar ga dukkan yankuna
- Kallo ya koma sama don ganin yadda PDP za ta yi da tikitin takararta na shugaban kasa bayan bayyanar dan takarar Ciyaman na jam'iyyar ta kasa
- Wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar sun nemi a bude tikitin takarar shugaban kasar jam'iyyar ga dukka yankunan kasar
- A bisa al'ada, PDP ta kan mika shugabancinta da kujerar shugaban kasa ga yankuna daban-daban
A ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, Satana Iyorchia Ayu, ya bayyana a matsayin dan takarar shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Ayu ya fito daga jihar Benue a arewa ta tsakiya.
Yayin da yankin arewa ke kan ga'bar samar da shugaban PDP na kasa, masana lamuran siyasa sun yi hasashen cewa jam’iyyar na iya mika tikitin takarar shugaban kasarta zuwa yankin kudu.
Sai dai kuma, rahotannin jaridun The Nation da Punch sun nuna cewa wasu manyan mambobin PDP na so a bude wa kowa tikitin takarar shugaban kasa, wanda hakan na iya ba arewa damar fito da dan takarar shugaban kasa, duk da cewar ta samu kujerar Ciyaman na jam’iyyar.
A kasa ga jerin jiga-jigan jam’iyyar da ake zargin suna so a bude tikitin takarar jam’iyyar ga dukka yankuna:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
2. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki
3. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto
4. Tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido
5. Tsohon shugaban riko na jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Kawu Baraje
6. Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa
A gefe guda, mun kawo a baya cewa duk da bayyanar tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchia Ayu a matsayin dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar PDP gabannin babban taronta, Kawu Baraje ya bayyana cewa an amince wa arewa ta shiga takarar shugaban kasa na 2023.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Baraje, wanda ya kasance tsohon shugaban PDP na kasa, ya ce jam’iyyar ta ba arewa damar samar da dan takarar shugaban kasarta a 2023 duk da bayyanar dan arewa, Sanata Iyorchia Ayu.
Legit.ng ta tattaro cewa Baraje ya tabbatar da hakan ne a yayin wata hira da jaridar a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng