2023: Bayan samun ƙarin mutum biyu, yan takarar dake hangen kujerar Buhari a PDP sun kai 15
- Bayan karin mutum biyu sun shiga takara, adadin masu neman gaje shugaba Buhari a 2023 karkashin PDP ya kai 15
- Bayanai sun nuna cewa dukkan yan takara 15 ɗin sun cake kudi Miliyan N40m sun siya Fam, jumulla miliyan N600 kenan
- Jam'iyyar PDP mai hamayya ta ƙara wa'adin siyar da Fam ɗin nuna sha'awa, hakan ya sa ta samu kari
Abuja - Adadin yan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP sun kai 15 bayan siyan Fam ɗin sha'awar takara da Cosmos Chukwudi Ndukwe ya yi.
Kafin PDP ta ƙara wa'adin siyar da Fam ɗin, mutum 13 ne kacal suka lale Miliyan N40m suka sayi Fam ɗin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Amma adadin ya ƙaru bayan ɗaukar matakin ƙara wa'adin, biyo bayan siyan Fam na farko da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, yayi, daga bisani Ndukwe ya mara masa baya.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan Fam ya zo hannunsa ranar Litinin, Ndukwe, ya ce a matsayin tsohon shugaban ma'aikata, kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar Abia, yana da kwarewar shawo kan matsalolin ƙasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ɗan takarar ya ce ya shirya tsaf wajen ceto Najeriya, ya miƙa ta hannun mutane, asalin waɗan da suke cancanta da ita.
A kalamansa ya ce:
"Da zaran an fara tafiya da mutane a dukkan harkokin gwamnatin Najeriya, da tsarin ƙasar mu, daga nan zata fara dawowa hannun su, ta tsira."
"Ina tunanin lokaci ya yi da mutane zasu dawo bayan mu, waɗan da suka shaida matsanancin halin da ake ciki wajen kwato ƙasar mu daga hannun da take, saboda kullum ƙasar nan kara baya take, ta kama hanyar karewa"
Dole a ba ɗan kudu-gabas kujerar shugaban ƙasa - Obi
Tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya ce ya zama wajibi a bar yankin kudu maso gabas ya fitar da shugaban ƙasa na gaba.
Ya kafa hujjar cewa matukar ana son kwatanta adalci, daidaito da kuma girmama yankin, to wajibi a zaƙulo wani Ibo ya zama shugaban ƙasa a 2023.
A wani labarin kuma Wasu Jiga-Jigan PDP biyu da daruruwan mambobi sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Oyo
Wasu manyan jiga-jigan PDP a jihar Oyo sun ja dandazon masoyan su zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.
Ɗaya daga cikinsu, tsohon ɗan takarar gwamna, Mista Popoola, ya ce laimar PDP ta tsage kuna jam'iyyar ba zata iya katabus ba a Oyo.
Asali: Legit.ng