2023: Ku bani tikitin shugaban ƙasa zan kwato mana mulki, Gwamnan Arewa ya roki PDP
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya roki PDP ta tsayar da shi takara zai lallasa kowa ya zama shugbaan kasa a 2023
- Tambuwal ya ce idan ya samu nasara mambobin PDP zasu amfana, domin zai naɗa su mukamai manya-manya
- A cewar Tambuwal wajibi PDP ta natsu, ta yi tsari mai kyau domin samun nasara a zaɓe mai zuwa
Sokoto - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, ya roki jam'iyya ta duba yiwuwar tsayar da shi takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Tambuwal ya ce matukar PDP ta ba shi tikitin takara to zai share mata hawaye ya dawo mata karagar mulkin Najeriya, kamar yadda Punch ta rahoto.
A cewar gwamnan jihar Arewa da zaran ya zama shugaban kasa zai ɗakko mambobin jam'iyya ya naɗa su manyan mukamai.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Muhammad Bello, kuma aka raba wa manema labarai.
A cewar sanarwan, Tambuwal ya yi rokon ne yayin ganawa da tsofaffin yan majalisu a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.
Gwamnan ya faɗakar da PDP ta canza tunani game da tsarin karɓa-karba, ka da ta ce dole sai ɗan wani yanki zata tsayar takara, wanda wasu ke goyon bayan haka.
Ya kuma tuna wa jam'iyyarsa matakin da APC ta ɗauka na watsi da zancen yanki, suka kai takara jihar Katsina, inda mariyayi Umaru Musa Yar'adua, ya fito.
A sanarwan, gwamnan ya ce:
"Zamu iya raba tikitin amma wajibi mu yi tsarin da zamu ci nasara, tilas PDP ta rungumi abin da ke zahiri."
"Dole a baiwa kowa haƙƙinsa, domin tsarin yanki-yanki, musulmi da musulmi ko Kirista da Kirista ba zai kaimu ga gaci ba, zai haifar mana da wani bal'i ne kawai."
Yadda zamu lashe zabe a 2023 - Tambuwal
Gwamnan Sokoto ya kuma bayyana hasashensa kan hanyoyin da jam'iyyar PDP zata bi ta samu nasara a babban zaɓen shugaban ƙasa ɗake tafe a 2023.
Ya ce APC na da ƙarfi a arewa da gwamnoni 16, haka PDP tana da ƙarfi a Kudu,dan haka wajibi PDP, "ta yi tunani mai kyau, tsari mai kyau kuma ta lashe zaɓe."
A wani labarin kuma Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa
Tsohon Sakataren jam'iyyar APGA ta ƙasa, Dakta Sani Shinkafi, ya janye daga tseren takatar shugaban APC na ƙasa.
Jigon siyasan wanda ya koma APC tare da gwamna Matawalle, ya ce ya yi haka ne domin biyayya ga matakin jam'iyya.
Asali: Legit.ng