Gwamnan Arewa zai fara neman shawara kan ko ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023
- Gwamnan jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya ya ce ya amince ya fara neman shawarin iyayen ƙasa kan neman takara a 2023
- Aminu Tambuwal ya nuna sha'awar neman kujera lamba ɗaya a Najeriya bayan gana wa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Sokoto
- Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, na daga cikin masu neman takara karkashin PDP
Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, a ranar Litinin, yace zai fara neman shawari kan ko ya dace ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe ko kuma akasin haka.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana sha'awar neman takara a babban zaɓen dake tafe ranar Litinin 31 ga watan Janairu, 2022.
Tambuwal ya yi wannan furucin ne yayin wani taro da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyarsa ta PDP a jihar Sokoto.
Ya ƙara da laƙaito cewa kafin ya nemi kujerar shugaban majalisar wakilai ta tarayya a shekarar 2011, sai da ya nemi shawarin manyan mutane.
Ya tabbatar da cewa sai da ya nemi shawarin mutane irin su tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Shehu Shagari, da kuma wasu iyayen ƙasa.
Leadership ta rahoto Gwamna Tambuwal ya ce:
"Na amince da kiran da kuke mun, kuma da yardar Allah (SAW) zan fara neman shawari kan kudirin daga yanzun har zuwa watan Fabrairu, 2022."
Mutanen dake neman takara a PDP
Gwamna Tambuwal ya shiga jerin masu fafutukar samun tikitin PDP tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Sauran sun haɗa da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, da fitaccen ɗan jaridar nan, Dele Momodu.
A wani labarin na daban kuma Mutane sun mutu a wani sabon Hatsarin Jirgin ruwa da ya sake aukuwa a jihar Kano
Akalla mutum biyu aka tabbatar sun rasu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya sake faruwa a ƙaramar hukumar Rimin Gado, jihar Kano.
Rahoto ya bayyana cewa Kwalekwalen mai ɗauke da fasinjoji ya kife ne a hanyarsa daga ƙauyen Zangon Durgu zuwa Kanya.
Asali: Legit.ng