Buba Galadima: Dalilan da suka sa ake ta kame-kame, aka ki amincewa a gyara dokar zabe
- Buba Galadima yace son kai ya sa Muhammadu Buhari ya ki yarda da kudirin gyara dokar zabe
- A cewar Injiniya Buba Galadima, shugaban kasar ya yi haka ne domin ya kare kansa da gwamnatinsa
- ‘Dan siyasar yace na-kusa da Buhari ne suka ba shi wannan shawara saboda tsoron za su fadi zabe
Abuja - Injiniya Buba Galadima ya yi wata hira da BBC Hausa a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, inda ya yi maganar kudirin gyaran zabe.
Buba Galadima ya bayyana cewa dama can ya san ba za a amince kudiri ya zama doka ba, saboda son kan na-kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Na yi magana a kafofin labarai da yawa, wanda na ce idan har (Buhari) ya yarda ya sa hannu a kudirin, to ni na yarda a fille mani kai.
Domin na yi imani cewa ba zai sa hannu ba, saboda wasu dalilai. Ba domin al’umma ba, don kariyar kan shi da gwamnatinsa kurum.
Babban dalili shi ne, a cikin masu ba shi shawara, akwai wadanda suke da sha’awa a kan wannan doka, domin su na jin za su rasa bukatunsu.
Na biyu, su na nuna masa cewa dama can su na cin zabe ne ba don yawan kuri’a ba, sai saboda karfin murdiya na hukuma da jami’an tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Buba Galadima
Buba Galadima ya bayyana cewa an fi shekara biyu wannan kudiri ya na ta faman sintiri tsakanin fadar shugaban Najeriya da majalisar tarayya.
Da farko ‘dan siyasar yace gwamnatin APC ta fake da cewa Bukola Saraki ne ya shirya tuggu, amma a zahiri ana tsoron jam’iyyar APC za ta fadi zabe ne.
Har ila yau, Galadima ya kara da shaidawa BBC cewa ko da za a cire sassan kudirin da ake kuka a kai, shugaba Buhari ba zai yarda ya rattaba hannunsa ba.
Buba Galadima yace APC na tsoron fadi zabe
“Muddin aka yi sahihin zabe, ina tabbatarwa mutane, ko kansila daya jam’iyyar APC ba za ta ci ba a kasar nan, idan sun isa, su sa hannu a dokar.”
A karshe Galadima ya karyata uzurin da ake badawa na cewa kudirin zaben zai kawo wasu matsaloli, yace kin yarda da kudirin ya taba kimar Buhari.
Hasashen da Sanata Kwankwaso ya yi
A baya an ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa ya yi imanin Buhari ba zai sa hannu kan kudin gyaran dokar zabe ba.
Sanata Kwankwaso ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohi ne suka matsawa Shugaban kasa a kan wannan batun, su ka ba shi shawara ya yi fatali da kudirin.
Asali: Legit.ng