Buhari Ya Yi wa Sheikh Pantami Wasa da Dariya da Ya Ziyarce Shi a Kaduna

Buhari Ya Yi wa Sheikh Pantami Wasa da Dariya da Ya Ziyarce Shi a Kaduna

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi manyan baƙi a gidansa da ke Kaduna ranar Juma'ar nan
  • Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami sun kai masa ziyara
  • Murmushi da hirar wasa da dariya tsakanin Buhari da Pantami ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - A ranar Juma'a, 11 ga Afrilu, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi manyan baki a gidansa da ke Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa cikin bakin da suka ziyarce shi har da tsofaffin ministocinsa biyu – Sheikh Isa Ali Pantami da Abubakar Malami, SAN.

Pantami
Buhari ya yi barkwanci a lokacin da Pantami ya ziyarce shi. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan abin da ya faru a lokacin ziyarar ne a cikin wani sako da Sheikh Pantami ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majidadin Daular Usmaniyya, Sheikh Pantami ya bayyana cewa sun yi ziyarar ne domin yi wa Buhari gaisuwar Sallah.

A wata sanarwa da ya wallafa, Pantami ya ce:

“Mun kai gaisuwar Sallah ga mai girma Baba Buhari tare da Abubakar Malami, SAN, CON a yau. Allah ya karɓi ayyukan alherinmu a cikin Ramadan da bayan sa.”

Hirar wasa da dariya tsakanin Pantami da Buhari

A lokacin ziyarar, Buhari ya yi dariya yana kallon Sheikh Pantami sannan ya ce:

“Hahaha... Akramakallah, ka murmure sosai fa.”

Pantami kuwa cikin girmamawa ya amsa da cewa:

“Alhamdu lil Laahi, Baba.”

Bayan kammala ziyarar, Sheikh Pantami ya gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Yahya Road da ke Kaduna.

Tsohon ministan ya ce:

“Na gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Yahya Road, Kaduna, a yau. Allah ya karɓi ayyukan alherinmu.”
Pantami
Pantami yana gabawa da Buhari. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Ra'ayoyin jama'a kan rahar Buhari

Barkwancin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi ya haifar da martani iri-iri daga al’umma a kafafen sada zumunta, musamman a rubutun da Sheikh Pantami ya yi a Facebook.

Kara karanta wannan

'Matsalar da za ka fuskanta idan Buhari bai tare da kai': An tsoratar da Tinubu

Cikin dariya Nana Zainab Umar ta ce:

“Murmurewar ce damuwarsa.”

Abubakar Nafiu Daura ya ce:

“Akwai soyayya. Sai dai duk zumunci Malam da Baba Buhari, Malam bai taɓa gabatar mana da lakca a Daura ba ko sau ɗaya.
"Sheikh Professor Isa Ali Pantami, mu mutanen Daura masoyanka ne. Mu ci albarkacin Baba mana.”

Suleiman Idris ya rubuta cewa:

“Masha Allah Sheikh. Allah ya ƙara lafiya, ilimi, baiwa, imani da falala. Ya sa mu yi ƙarshe mai albarka, ya kuma yi wa iyayenka da namu rahama. Ameen.”

Muh’d Hafiz Hussein ya nuna wata fuska da cewa:

“Kila fa bai ji daɗin murmurewar ba.”

Hajara Ismail kuwa ta yi fatan alheri da cewa:

“Allah ya nuna mana rana da shi ma Baba Buhari zai kawo ma Akramakallah ziyarar taya murnar zama shugaban ƙasan Najeriya.”

Atiku ya ziyarci Buhari a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi Atiku Abubakar a gidansa na Kaduna.

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari

Atiku Abubakar ya jagoranci wata babbar tawaga da ta hada da tsofaffin gwamnoni da suka hada da Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna.

Duk da cewa ana ganin kamar ziyarar na da alaka da siyasa, Atiku Abubakar ya ce ya kai ziyarar ne domin yi wa Buhari gaisuwar sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng