Bidiyo: Budurwa ta Tada Komadar Mahaifiyarta, Ta Koma Budurwa Sharaf da Kwalliya
- Bidiyon wata tsohuwar mata da 'diyarta ta sanya mata kaya ya jawo cecekucen masu amfani da yanar gizo
- Tsohuwar matar ta bayyana ne a bidiyon kamar wata karamar yarinyar yayin da take takawa 'dai'dai kamar wata tauraruwa
- 'Yan soshiyal midiya sun yaba da shigarta yayin da suke ta jinjinawa kyakyawar alakar da ke tsakaninta da 'diyarta
Masu amfani da kafar sada zumuntar zamani sun bayyana ra'ayoyinsu game da wani faifan bidiyon da ke nuna yadda wata 'diya ta maida tsohuwar mahaifiyarta karamar yarinya.
Kamar yadda a @_vickyb ta wallafa a dandalin TikTok ranar 24 ga watan Disamba, tsohuwar ta bayyana ne a sutura mai kama jiki na 'diyarta yayin da take takawa 'dai'dai kamar wata karamar yarinya.
A bidiyon, da farko dai an ga matar a buje da riga. Daga bisani, ta bayyana a riga mai kama jiki da wasu takalma masu tsini. Tsohuwar matar mai ban sha'awa ta sanya hular gashi a kanta don cikasa wankanta.
Mutane da dama sun yi tsokaci game da bidiyon inda suke cewa ta matukar 'kayatarwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Martanin jama'a
@AwOriginals ta ce:
"Yanzu dai in koya wannan salon ne gaba daya daga tsohuwa wacce ta fara wanka kamar karamar yarinya."
@Juice ta ce:
"TANA BOYE DUK WANNAN."
@Ashley Williamceau ya ce:
"Mahaifiyata wacce ba ta zamani ba za ta tsine min idan na bukaci tayi haka."
@elisha ta ce:
"Ita da wannan rigar sam basu dace ba."
@da.dene ya ce:
"Kada kayi wasa da wannan yarinyar, ba ta daga cikinsu!!!!."
@Bambi ta ce:
"Kai ji yadda tayi kyau a iya zabge shekaru 10 daga nata."
Bayan shekaru 16 a Dubai, budurwa ta dawo neman miji Najeriya
A wani labari na daban, wata kyakyawar budurwa ta dawo gida Najeriya bayan kwashe shekaru 15 a birnin Dubai dake Haddaiyar Daular Larabawa.
Budurwar wacce ta sanar da cewa biyan kudin haya take yi koda tana wurin uwar dakinta ne a Dubai din, tace ta gaji shiyasa ta dawo Najeriya.
Amma ta sanar da cewa manufar ta ita ce ta samun mijin aure nagari wanda zasu rufawa juna asiri su yi aurensu tare da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng