Bidiyon Yadda Kare Ya Hau Sama, Ya Janyo Kusan N900k Ya Yagalgala
- Wata mata ta shiga cikin tashin hankali yayin da karenta ya cinye mata kusan $2000 ( N893,260) wanda ta bari kan tebiri lokacin da za ta fita
- Yadda ta kacaccala mata dalolin kan kujera, tebiri da wasu a kasa, matar bata iya rike hawayenta ba bisa barnar da ta mata
- 'Yan dandalin TikTok da dama sun yi kokarin tausarta yayin da wasu suke tunanin ko wani banki zai ya taimakawa wajen canza mata kudin.
Wata mata, @kimkruk tana nadamar barin karenta shi kadai a gidan na tsawon wasu awanni. Ta dawo tare da ganin yadda ya kacaccala mata kusan duka kudin ta.
A wani bidiyo da ta bayyana tana kuka, matar ta bayyana yadda karen nata ya haura inda kudin suke tare da cinye kusan $2000(N893,260). Karen ya zuba mata ido, ba tare da sanin ya cinye mata makuden kudi ba.
Bidiyon matar da karen ya janyo cece-kuce. Yayin da wasu suka roki matar ta yafewa karen, sai dai wasu mutane sun ce dabbar na alfahari da abun da yayi.
Yayin da matar ke kuka, ta hasko kamarar wayarta daga fuskarta dauke da hawaye zuwa yagaggun kudaden da karen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a sun yi martani
Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya tattara tsokaci 42,000 da dubbannin jinjina.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin kamar haka:
lil ya ce:
"Wannan ya koyar da darasi mara dadi."
scruffyleartist ya ce:
"Alamu sun nuna yadda take alfahari da kanta da farin cikin barnar da tayi."
Donald ya ce:
"Gaggauta siyar da karen nan ya kamata a yi."
Gretagris yayi tambaya:
"Me yasa baki bar lafiyayyu 2 ba kawai a kan tebirin?"
Normalinda ya ce:
"Wannan tarin kudi... banki za su canza miki idan kina da sama da kashi 3 cikin 4 na kudin."
redfish0511 ya ce:
"Na san da ban takaici amma karen ki yafi kudi kuma yana kaunarki!?"
Bayan kwashe shekaru 15 a Dubai, budurwa ta dawo Najeriya neman miji
A wani labari na daban, wata budurwa ta bayyana a bidiyon inda tace ta dawo Najeriya bayan kwashe shekaru 15 a birnin Dubai.
Ta sanar da cewa ta bazama Najeriya neman mashinshini ne.
Asali: Legit.ng