Shatta Wale: Na gwammace in 'watsa' kudi na a titi maimakon bawa coci a matsayin sadaka

Shatta Wale: Na gwammace in 'watsa' kudi na a titi maimakon bawa coci a matsayin sadaka

  • Wani mawakin kasar Ghana, Charles Mensah wanda aka fi sani da Shatta Wale ya bayyana ra’ayinsa inda ya ce gara ya watsa kudinsa a titi akan ya mika su matsayin sadaka a coci
  • Ya yi wannan furucin ne yayin da ake tattaunawa da shi a wani gidan rediyo inda ya ce Ubangiji ya taimake sa kwarai har ya samu ya kai matakin da yake
  • A cewarsa, ya yarda kwarai da masoyansa da ke kan hanya, hakan ya sa ya gwammaci ya rarraba kudi a titi akan ya mika su a matsayin sadaka a coci

Ghana - Wani mawakin kasar, Charles Mensah wanda aka fi sani da Shatta Wale ya bayyana ra’ayinsa inda ya ce ya gwammaci ya watsa kudi a titi akan ya mika su sadaka a coci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Talaka ya tsinci katuwar wayar salula, ya dawo da ita, ya nemi a ba shi tukwucin N1500 kacal

A wata hira ta gidan rediyo da aka yi da shi, mawakin ya ce Ubangiji ya taimaka masa kwarai har ya samu daukakar da yake ciki yanzu haka, don haka ya ke ba masoyansa muhimmanci.

Gara in watsar da kuɗi na a titi maimakon in miƙa su coci, Shahararren mawaƙi, Shatta Wale
Shatta Wale: Da in bawa coci sadaka, gara na watsar da kudi na a kan titi. Hoto: Shatta Wale
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Mutane da dama su na fadin maganganu a kai na amma abinda ka ke tunani a kai na yana da bambanci akan yadda wasu suke kallo na... akwai wani, a wani wuri da yake son tallafa wa Shatta Wale a ko wanne yanayi don idan naje wasu wuraren tunani iri-iri ke zuwa min.”

Gara ya watsa kudi a titi

Mawakin na kasar Ghana ya kara da cewa ya yarda da masoyansa, Daily Trust ta ruwaito inda ya ce:

“Na sha fada wa kaina cewa da in mika sadaka coci, gara in watsa kudin a titi.”

Kara karanta wannan

Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

Shatta Wale wanda daya ne daga cikin manyan mawakan da kasar Ghana take ji da shi ya samu jinjina ta musamman a shekarar 2014 a taron jinjina wa mawakan Ghana na Vodafone.

Ana matukar girmama shi a masana’antar waka ta Ghana.

Sai dai sakamakon wata hayaniya da ta shiga tsakaninsa da ma’aikatar mawakan Najeriya,an yi ta surutai inda duk ya fita daga zuciyar ‘yan Najeriya.

Sun samu matsala da Burna Boy

Yayin da yake waka a wani dakin taro a Ghana yace:

“Sun ce min saboda ni mutane ba za su cika dakin taron nan ba. Babu wani banzan mawakin Najeriyan da na dogara da shi, da masoya na kawai na damu. Allah wadaran Najeriya”.

Shatta Wale ya je har shafinsa na Instagram inda ya kira wasu mawakan Najeriya kamar Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy inda ya zarge shi da yin gulmarsa a Ghana.

Kamar yadda ya ce:

Kara karanta wannan

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

“Na kusa zuwa in bayyana yadda Burna Boy ya tafi yana surutan banza a kaina, maimakon ya fuskance ni ya yi min magana. Da na rike shi da ya shiga uku... Wawayen mutane.”

Shahararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba

A wani labarin daban, shahararren mawakin Najeriya Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid ya bayyana cewa shi bai yi imani da addini ba, Daily Trust ta ruwaito.

Balogon ya bayyana hakan ne cikin wata wallafa da ya yi a dandalin sada zumunta ta Snapchat.

Ya ce:

"Bana tashi daga barci da bakin ciki, bana farka wa cikin talauci a rayuwa, cikin koshin lafiya da kyakyawar ruhi kuma bana tashi da kiyayya a zuciya ta.
"Kada ka bata rayuwar ka kan abubuwa masu wucewa. Ka more rayuwa, shekaru ba ya nuna cewa kana da basira, na san mutane masu shekaru sosai amma ba su da hankali kuma ban yi imani da addini ba."

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164