Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya aiko takardar sallama ga King Indara don wallafe-wallafen da ya yi masu cike da rashin da'a ga Abba Kabir.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya aiko takardar sallama ga King Indara don wallafe-wallafen da ya yi masu cike da rashin da'a ga Abba Kabir.
Mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya kare gwamnatin Bola Tinubu game da tsadar man fetur da ake a Najeriya, inda ya ce ana kukan dadi ne a fadin kasar.
A labarin nan, za a ji irin shirin da gwamnatin tarayya ta yi wajen karrama marigayi tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari bayan cikarsa shekara da rasuwa.
Rahotanni sun ce akalla sojoji 2 sun rasa rayukansu a hanyar zuwa kai dauki yayin da bam da tarwatse da motarsu a yankin karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato.
An tabbatar da rasuwar wani kwararren likita, Dr. Ibrahim jim kadan bayan ybiza asibiti domin far duba marasa lafiya a jihar Kano ranar Asabar da ta wuce.
A labarin nan za a ji cewa hukumar Tattara Kudin Shiga, Raba Kasafi da Kula da Albashi (RMAFC) ta dauki turbar karin albashi ga masu rike da mukaman gwamnati.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya nada mai magana da yawun shi, Kenneth Okonkwo yayin da ake shirin babban zaben 2027.
Olusegun Obasanjo ya ce ba ya fatan sake faruwar yakin basasa a Najeriya. Ya ce abin tsoro shi ne har yanzu ba magance abubuwan da suka haifar da yakin ba.
Fasahar da aka kawo za ta ba jama'a damar sauke katinsu na PVC. Kuma daga nan gaba kadan, babu maganar ziyartar ofishi ko cibiyoyin rajista kafin a samu PVC.
Fadar shugaban kasa ta zargi Adeniyi Adeyemi da kafa ma'aikatar bogi a Najeriya ba tare da sanin shugaban kasa Bola Tinubu da sauran hukumomin Najeriya ba.
Mazauna kauyen Dansarai a Katsina sun yi artabu da ‘yan bindiga, inda aka kashe mutane hudu tare da fatattakar maharan. An ce 'yan bindiga sun tsere da suka ji wuta.
Labarai
Samu kari