Obasanjo Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Hanyar Gyara Najeriya
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi tsokaci kan kalubalen da Najeriya ke fsukanta kala-kala
- Olusegun Obasanjo ya ba da shawara kan hanyar da yake ganin za a bi domin a gyara kasar yadda ya kamata
- Tsohon shugaban kasar ya kuma nuna cewa yana da a kyau a rika saka matasa a cikin harkokin mulki dumu-dumu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ɗauki alhakin gina makomar ƙasar baki ɗaya.
Obasanjo ya yi gargaɗin cewa samun ci gaba mai ma’ana zai ci gaba da kasancewa abu mai wahala har sai idan ’yan Najeriha sun haɗa kai don magance ƙalubalen ƙasar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026 yayin taron ƙara wa juna sani na shekara-shekara karo na shida.
An gudanar da taron ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar wanda ya kafa cocin Trinity Church, Fasto Itua Ighodalo, mai shekaru 65, tare da taken: “Makomar Najeriya.”
Me Obasanjo ya ce kan gyara Najeriya?
Tsohon shugaban ƙasar, wanda Farfesa Adedeji Daramola, mataimakin babban jami’in gudanarwa na cibiyar shugabanci ta Olusegun Obasanjo ya wakilta, ya jaddada cewa gina ƙasa wani babban aiki ne da ya shafi dukkan ɓangarorin al’umma.
"Har sai idan mun haɗu don magance wannan matsalar, babu yadda za mu zauna kawai muna jiran mu’ujiza ta faru."
“Kowa yana da rawar da zai taka. Alhaki ne na dukkanmu baki ɗaya. Makomar Najeriya tana da kyau duk da ƙalubalen da ake ciki yanzu."
"Kowane ɗan ƙasa, tun daga kan matan kasuwa zuwa ƙwararru a fannoni daban-daban da kuma shugabannin siyasa, dole ne su ba da tasu gudunmawar wajen fito da hanyar da ƙasar za ta bi.”
“Dole ne sai mun haɗu don yin aiki da gyara Najeriya, domin babu wanda zai gyara mana ita.”
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya ba da shawara
Obasanjo ya lura cewa ko da yake shugabanci yana da matuƙar muhimmanci, babban al’amarin yana ga yadda dukkan jama’a za su saka hannu da kuma ɗaukar nauyi.
Haka zalika, ya jaddada buƙatar sanya matasa dumu-dumu a cikin harkokin mulki da hanyoyin ci gaba, inda ya bayyana su a matsayin jigon makomar Najeriya.

Source: Facebook
Taron ya samu halartar manyan baki, da suka haɗa da mawallafin jaridar Vanguard, Sam Amuka, mace mafi arziki a Afirka, Folorunsho Alakija, da Donald Duke, da sauran su, waɗanda suka taru domin karrama Fasto Ighodalo.
Baki ɗaya, mahalarta taron sun amince cewa Najeriya tana cikin wani yanayi mai muhimmanci, inda ɗaukar kyakkyawan mataki, shigar da kowa a mulki, da kuma zuba jari ga matasa da ababen more rayuwa su ne za su tabbatar da makomar ƙasar a duniya.
Obasanjo ya yi magana kan rikicin Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan rikicin Boko Haram.
Obasanjo ya bayyana takaicin yadda aka kwashe shekaru15 ana yakin Boko Haram, wanda ya fi tsawon yaki basasa da aka yi daga 1967 zuwa 1970.
Tsohon shugaban kasar ya ce lokaci ya yi Najeriya za ta hada kai da sauran kasashe domin koyo dabarun yaki da barazana irin Boko Haram.
Asali: Legit.ng

