Matakin da Amurka Za Ta Dauka idan Gwamnati Ta Gaza Magance Kashe Kashe a Najeriya
- Dan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Republican, Riley Moore, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a Najeriya
- Riley Moore ya nuna damuwa kan karuwar kashe-kashe da rikici a wasu sassa na Najeriya, inda ya nuna cewa Amurka na shirin daukar mataki
- Dan majalisar ya nuna cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta daukar matakan da suka dace cikin hanzari domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Wani ɗan majalisar wakilai na Amurka, Riley Moore, ya yi gargaɗi kan kashe-kashe a Najeriya.
Riley Moore ya yi gargadin cewa Amurka na iya shige wa gaba wajen tunkarar matsalar tsaron Najeriya idan hukumomin ƙasar suka gaza yin hanzari wajen dakatar da kashe-kashen da ake yi.

Source: UGC
Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da tashar Newsmax a ranar Laraba, 1 ga watan Afirilun 2026.
Riley Moore ya mika rahotonsa
Riley Moore ya ce rahoton da ya miƙa wa fadar White House a watan jiya ya zayyana "kwararan matakai" na tunkarar abin da ya bayyana a matsayin ƙaruwar tashe-tashen hankula kan Kiristoci a Najeriya.
“Wannan rahoton da muka gabatar wa fadar White House ya biyo bayan buƙatar da Shugaban ƙasa ya yi mini ne da kuma Tom Cole… domin mu binciki wannan tsananta wa Kiristoci da kuma abin da nake kira kisan ƙare-dangi a Najeriya."
- Riley Moore
Dan majalisar Amura ya koka rashin tsaro
Riley Moore, wanda ya ziyarci Najeriya kwanan nan, ya ce ya ga halin da ake ciki da idonsa.
“Mun je can. Na gani da idona, masifa da abubuwan ban tsoro da ke faruwa a can."
- Riley Moore
Wane mataki Amurka za ta dauka?
Riley Moore ya yi gargaɗin cewa Washington na iya ƙara kaimi wajen shiga tsakani idan hukumomin Najeriya suka gaza daukar matakan da suka dace.
"Kamar yadda Shugaba Trump ya bayyana hakan a fili, idan ba su magance wannan ba, mu ne za mu magance musu shi."
“Muna son yin hakan ta hanyar haɗin gwiwa da tsari, amma idan ba su tashi tsaye ba, mu ne za mu jagoranci lamarin.”
"Gwamnatin Najeriya tana ƙoƙarin ɗaukar wasu matakai game da lamarin, amma ba sa yin hakan cikin sauri yadda ya kamata."
"Abubuwa ba sa tafiya da hanzari, kuma waɗannan tashe-tashen hankula na ci gaba da faruwa. Dole ne a samu wani gagarumin sauyi."
- Riley Moore

Source: Twitter
A halin yanzu, Amurka tana da dakarun sojoji kusan 200 a Najeriya waɗanda ke ba da horo da bayanan sirri ga dakarun Najeriya.
Shugaban Iran ya aika wasika ga Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya aika da budaddiyar wasika ga Amurka.
Shugaba Pezeshkian ya yi fatali da yadda ake nuna Iran a matsayin barazana ga tsaro, yana mai cewa hakan daidai ba ne.
Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa a tarihin Iran na tsawon zamani, ba ta taɓa zaɓar hanyar ta’addanci, mamaya, mulkin mallaka, ko danniya ba.
Asali: Legit.ng

