Abin da Ministan Tsaro Ya Fada wa Sojojin da ke Arangama da 'Yan Ta'adda a Borno
- Ministocin tsaro sun ziyarci hedikwatar 'Operation hadin kai' da ke fafata wa da yan ta'adda a Maiduguri na jihar Borno
- Sojoji sun kashe sama da ‘yan ta’adda 280 a lokacin azumin watan Ramadan, duk da munanan hare-hare da aka kawo masu
- Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo karshen ta’addanci tare da sanar da sojojin shirin da aka yi domin taimaka masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Ministan tsaro, Christopher Musa tare da karamin Ministan tsaro na kasa, Bello Matawalle, sun kai ziyara hedikwatar 'Operation hadin kai' da ke Maiduguri a jihar Borno.
Dukkanin Ministaocin sun yi magana game da halin rashin tsaro da ake ciki da manufar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta a kan matsalar.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa Ministocin sun kai ziyarar ne domin duba yadda ake gudanar da ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da kuma tantance ci gaban da aka samu a yankin Arewa maso Gabas.
Ministoci sun yaba da kokarin sojoji
Jaridar Punch ta wallafa cewa da yake zantawa da manema labarai, Christopher Musa ya yabawa rundunar sojojin Najeriya bisa gagarumin ci gaban da aka samu a yaki da ta’addanci.
Ya danganta nasarorin da aka samu da ingantacciyar hadin kai da kuma kwarewar jami’an tsaro da suke aikin wanzar da tsaro a yankin.
Ya kuma jaddada bukatar samun cikakken goyon bayan ‘yan kasa domin tabbatar da dorewar wannan nasara.
Ministan tsaro ya kara da tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na nan daram wajen magance matsalar tsaro a fadin kasar.
Minista ya yi magana da sojoji
A lokacin da suka gana da sojoji, ministocin sun isar da godiyar Shugaban kasa bisa sadaukarwar da suke yi, tare da karfafa masu gwiwa su ci gaba da matsa lamba kan ‘yan ta’adda.

Source: Facebook
A yayin ziyarar, ministocin sun kai ziyara makabartar sojoji da ke Maiduguri, inda suka ajiye furanni domin karrama jaruman da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Haka kuma, sun duba sabuwar cibiyar tsaro da aka gina domin inganta tattara bayanan sirri da kuma daidaita ayyukan soji.
An kuma kaddamar da sababbin gidajen zama ga sojoji domin kara inganta jin dadinsu da kwarin gwiwa.
Kwamandan rundunar, Abdulsalam Abubakar, ya yi wa ministocin karin haske kan halin da ake ciki a fagen daga.
Ya bayyana cewa sojoji sun kashe sama da ‘yan ta’adda 280 a lokacin watan Ramadan, tare da lalata hanyoyin samar da kayan aiki na ‘yan ta’adda da kuma ceto mutanen da aka sace.
Ya kara da cewa rundunar na ci gaba da matsa lamba kan ‘yan ta’adda ta hanyar hadin gwiwar hare-haren kasa da sama.
An fadi aikin sojojin Amurka a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta yi kira ga dakarunta da su kara sanya ido sosai yayin da ake shirin bikin Easter a ranar Litinin, 6 ga Afrilun 2026.
Kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya yi bayani game da irin tallafin da sojojin Amurka ke bayarwa duk da karin hare-hare da aka samu a sassan kasar.
Sojojin Amurka sama da 100 sun zo Najeriya ne tun a lokacin da aka fara maganar zargin kashe Kiristoci a karshe-karshen shekarar 2025 kuma har yanzu suna nan.
Asali: Legit.ng


