Ana cikin Shagalin Sallah, Wani Abin Fashewa Ya Yi Bindiga a tsakiyar Jama'a a Najeriya
Calabar, Cross River - Yayin da musulmin Najeriya ke ci gaba da shagulgulan Sallah, an samu wata fashewar gas a gidan man Fokex a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Lamarin ya auku a gidan mai na Fomex da ke kan titin Edibe Edibe a karamar hukumar Kalaba ta Kudu, a safiyar ranar Asabar, inda ta lalata dukiya mai darajar miliyoyin Naira.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto cewa gas din ya fashe ne da misalin karfe 9:40 na safe, inda shaidu suka bayyana cewa karfin fashewar ya girgiza gine-ginen da ke kusa, har wasu suka dauka kamar fashewar bam ne.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu asarar rayuka ba, amma mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar.
Rahoto ya nuna cewa an ba wasu agajin gaggawa a shagunan sayar da magunguna na kusa, yayin da aka garzaya da wasu asibitoci domin karin kulawa.
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda jami’an kashe gobara na jiha da na tarayya suka jinkirta zuwa wurin, har bayan fiye da awa guda da faruwar lamarin.
Gidan man yana cikin unguwa mai yawan jama’a, lamarin da ya sa fashewar ta shafi shaguna da gidaje da dama, inda mazauna da ‘yan kasuwa suka tsere domin tsira da rayukansu.
A yayin da jami’an agaji ba su iso ba, an ce wasu bata-gari sun yi anfani da damar wajen sace kayayyaki daga shagunan da abin ya shafa.
Rahotanni sun bambanta kan abin da ya haddasa fashewar. Wasu mazauna yankin sun zargi cewa wata kila wani kwastoma ne ya yi waya kusa da wurin zuba gas.
Sai dai wani mekanike mai suna Ekpenyong Sam, wanda ke aiki a kusa da wurin, ya danganta lamarin da matsalar lantarki ko kuma lalacewar kayan aiki.
‘Yan sanda sun dauki mataki
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce an tura jami’ai zuwa wurin domin shawo kan lamarin.
Ya kara da cewa ana kokarin hada kai da jami’an kashe gobara, ciki har da na Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), domin dakile gobarar da kuma dawo da tsaro a yankin.
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng
