Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu don Bukukuwan Karamar Sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu don Bukukuwan Karamar Sallah

  • Al'ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan wanda bayan kammala shi za a yi bukukuwan karamar Sallah na shekarar 2026
  • Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranakun hutu don bukukuwan karamar Sallah
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya fitar da sanarwar, ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da yin addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaba

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranakun hutun bukukuwan karamar Sallah ta shekarar 2026.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 19 ga Maris, da kuma ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu don murnar bikin ƙaramar Sallah, wadda ke nuna ƙarshen wata mai alfarma na Ramadan.

Kara karanta wannan

Azumi ya zo karshe, Sarkin Musulmi ya fitar sanarwa kan ranar karamar Sallah a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun karamar Sallah
Ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: @BTOOfficial
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya yi wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya.

Gwamnati ta ba da hutun Sallah

Ministan ya ayyana ranakun hutun ne ta hanyar wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikata cikin gida, Dr. Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Talata, 17 ga watan Maris 2026, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Yayin da yake miƙa saƙon gaisuwa da taya murna ga al’ummar Musulmi kan kammala azumin watan Ramadan lafiya, Ministan ya buƙaci Musulmi da su dore da kyawawan halaye na ƙauna, karimci, zaman lafiya, haƙuri, da sadaukarwa, waɗanda aka jaddada a lokacin watan azumin.

Minista ya ba 'yan Najeriya shawara

Haka kuma, ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na biki wajen yi wa kasa addu’ar dorewar zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba.

Ministan ya ƙarfafa gwiwar ‘yan ƙasa da su yi bukukuwan cikin natsuwa sannan su nuna ayyukan jin ƙai ga mabukata a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fara neman sauran ƴan ƙunar baƙin wake a Borno, an nemi daukin jama'a

Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta ci gaba da jajircewa wajen haɓaka haɗin kan ƙasa da zaman lafiya a tsakanin dukkan ‘yan Najeriya.

Gwamnati ta ba da hutun karamar Sallah
Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Hoto: @BTOOfficial
Source: Facebook

Karanta wasu labarin kan gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta gatanta ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fito da sabon tsarin giratuti don ma'aikatan da suka yi ritaya.

Sabon tsarin da majalisar zartarwar ta amince da shi zai ba ma'aikatan gwamnatin tarayya damar samun garatuti da ya yi daidai da kashi 100 cikin 100 na jimillar albashinsu na shekara guda.

A ƙarƙashin sabon tsarin, ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka yi aiki na aƙalla shekaru 10 za su karɓi giratuti idan sun yi ritaya, baya ga sauran alfanun da suke samu a ƙarƙashin tsarin fansho da ake amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng