Gwamna Abba Ya Waiwayi Mata, Ya Shirya Tsamo Miliyoyi daga Kangin Talauci

Gwamna Abba Ya Waiwayi Mata, Ya Shirya Tsamo Miliyoyi daga Kangin Talauci

  • Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta kaddamar da wani shiri da zai tallafa wa mata
  • A karkashin shirin, gwamnati za ta samar wa miliyoyin mata hanyoyin dogaro da kai domin rahe radadin talauci
  • Kwamishinan raya birane da karkara na jihat Kano ya bayyana cewa gwamnatin ta fara bada tallafi ga mata daga dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa za a samar wa mata miliyan shida hanyoyin dogaro da kai.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne yayin da jihar ta ƙaddamar da shirin samar wa mata agajin tattalin arziki (WEE) a hukumance.

Gwamna Abba zai ba mata jari a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan raya birane da karkara, Abdulkadir Abdulsalam, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin.

Kara karanta wannan

"Ba za mu lamunci cin amana da rashin biyayya a jihar Kano ba": Gwamna Abba Kabir

Gwamnatin Abba za ta ba mata jari

Wannan shiri na da nufin fitar da mata fiye da miliyan shida daga kangin talauci nan da shekarar 2029 ta hanyar inganta hanyoyin samun kuɗaɗe, horas da sana’o’i, da samar da damammakia fannin tattalin arziki.

Da yake jawabi a madadin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kwamishinan ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin wani babban ƙoƙari da ke nufin haɓaka ci gaba da kuma sanya mata a cikin harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.

Ya ce wannan manufa tana wakiltar ƙwaƙƙwaran alƙawari na gwamnatin jihar mai ci yanzu don ƙarfafa rawar da mata ke takawa a ci gaban tattalin arziki, a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ci gaba mai dorewa.

A cewarsa, wannan yunƙuri ya yi daidai da manufar ci gaba na gwamnan da ake kira "Our Commitment" wanda ta mayar da hankali kan shugabanci na gari ga kowa da kuma samar wa ‘yan ƙasa dama daidai wa daida, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei ya yi jawabin farko, ya faranta wa wadanda yakin Iran ya shafa

Tuni aka fara aiwatar da shirin

Kwamishinan ya lura cewa tuni gwamnati ta fara aiwatar da shirye-shiryen tallafawa mata a fadin jihar.

Gwamna Abba zai ba mata hanyoyin dogaro da kai a Kano
Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya bayyana cewa a ƙarƙashin ɗaya daga cikin waɗannan yunƙurin, kimanin mata 5,200 daga mazabu 484 da ke ƙananan hukumomin Kano 44 suna karɓar N50,000 kowane wata don tallafa wa ƙananan sana’o’i da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arzikin gidaje.

“Wannan shirin ba sadaka ba ne, a’a, wani tsari ne na ƙarfafa tattalin arziki da aka tsara don haɓaka kudin shigar iyali da kuma ƙarfafa mata su tsaya da ƙafafunsu wajen neman abin kai."

- Abdulkadir Abdulsalam

Gwamna Abba ya tsige shugaban ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tsige shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar daga mukaminsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Alhaji Abdullahi Musa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan muƙamin, yana mai yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.

Hakazalika, Gwamna Abba ya ba da umarnin maye gurbin Alhaji Abdullahi da babbar sakatariya mai kula da ayyukan gidaje da gudanarwa a ofishin sakataren gwamnati, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng