Tinubu ya Amincewa Yarbawa su Dauki 'Yan Sa Kai Don Kare Yankinsu Daga 'Yan Ta'adda

Tinubu ya Amincewa Yarbawa su Dauki 'Yan Sa Kai Don Kare Yankinsu Daga 'Yan Ta'adda

  • Sunday Igboho ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani sabon shirin tsaro domin magance matsalar ta’addanci a yankin Kudu maso Yamma
  • Yawan matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ake kira da a dauki matakan gaggawa don ceto jama’a
  • Igboho ya jaddada bukatar bin hanyoyin zaman lafiya wajen yakar ta’addanci tare da neman goyon bayan gwamnati ga tsaron al’umma

Ibadan, jihar Oyo — Sunday Adeyemo, tsohon mai fafutukar kafa kasar Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani shirin tsaro domin tunkarar barazanar ta’addanci a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Bayanan nasa na zuwa ne a wani bidiyo da wata babbar ‘yar a mutun Igboho, Abibat Amudat wadda aka fi sani da Lady-K, ta wallafa a ranar Juma’a 6 ga watan Maris.

Sunday Igboho ya ce Tinubu ya amincewa Yarbawa su kafa rundunar tsare yankinsu
Sunday Igboho ya ce Tinubu ya amince a kafa tawagar kare yankin Yarbawa | Hoto: @NigeriaStories
Source: Twitter

Igboho ya ce an samu goyon bayan shugaban kasa ne bayan sarakunan Yorubawa sun gabatar da wannan shawara ga shugaba Tinubu. Ana sa ran za a iya daukan kusan ‘yan sa kai 50,000 domin aikin.

Kara karanta wannan

Gbajabiamila da yaran Tinubu da suka rike amana yau ake damawa da su a gwamnati

Tinubu ya goyi bayan shirin tsaro a Kudu maso Yamma

Rahotanni sun nuna cewa matsalolin tsaro na kara karuwa a fadin Najeriya, musamman a Arewacin Najeriya da ake fama da yawan garkuwa da mutane.

Duk da cewa yawancin hare-haren suna faruwa ne a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, rashin tsaro kamar fashi da makami, garkuwa da mutane da rikice-rikice masu tashin hankali na kara yaduwa zuwa wasu yankuna har da Kudancin kasar.

A yankin Kudu maso Yamma kuwa, gwamnonin jihohin yankin sun riga sun kafa rundunar tsaro ta yankin da ake kira Amotekun domin taimakawa wajen magance wadannan matsaloli. Duk da haka, ana ganin akwai bukatar kara karfafa matakan tsaro.

Bayanan Igboho kan tsaro a Kudu maso Yamma

Da yake magana a wani taro, Igboho ya ce:

“Shugaba Tinubu yana son mu samu tsaro, kuma wannan shi ne abin da muke so domin iyalanmu. Sun shirya su samar da shi, kuma dole mu mara musu baya da gaske.”

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Ya kara da cewa:

“Tinubu kamar uba ne a gare mu. Kowa ya sani cewa muna tare da shi. Idan muka samu cikakken izini domin fara wannan shirin tsaro, dole mu aiwatar da shi da zuciya daya ba tare da aikata wani laifi ba. Ina tabbatar muku cewa Shugaba Tinubu zai yi kokari wajen samar da tsaro domin mu iya kare iyalanmu yadda ya kamata.
“Tinubu ya ce, ‘Na ba ku ‘yanci. Ku je ku rayu rayuwarku. Ku tattauna da magoya bayanku. Zan goyi bayan shirin tsaron da kuke so.’
“Amma ya kuma bayyana karara cewa kada mu cutar da Hausawa ko Fulani marasa laifi. Wadanda kawai ke da hannu a ta’addanci ne ya kamata a fuskanta. A matsayinsa na gwamnati, zai ba da goyon bayan da ake bukata domin wannan yunkuri.”

Kalli bidiyon:

Yadda Igboho ya yi shuhura a yankinsu

A baya, Igboho ya shahara ne kawai a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, amma daga baya ya zama sanannen mutum a fadin kasar bayan ya shiga tsakiyar rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kara karanta wannan

Malamai sun yi magana, sun fadi yadda yakin Iran da Amurka ya shafi Najeriya

Rikicin da ke tsakanin makiyayan Fulani da wasu kungiyoyi kan batun filaye da kiwo a yankin Kudu maso Yamma ne sanadin shuhuran Sunday Igboho.

A yanzu haka, Igboho na da magoya baya da suka hada da wasu manyan ‘yan siyasa, sarakuna da shugabannin addini, kuma ana yawan ganinsa tare da su a wuraren taro na jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng