Kotu Ta Amince da Bukatar Abubakar Malami da Dansa, Ta Kafa Sharadi
- Tsohon Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya sake gurfana a gaban kotu tare da dansa
- Hukumar DSS ce dai ta gurfanar da Abubakar Malami tare da dansa a gaban kotun kan zargin daukar nauyin ta'addanci
- A yayin zaman kotun na ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta ba da belin mutanen guda biyu tare da kafa sharadi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami.
Kotun ta ba da belin Malami ne tare da ɗansa Abdulaziz, a kan kuɗi Naira miliyan 200 kowannensu, kan zarge-zargen da suka shafi ta’addanci.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce alkalin kotun, Mai shari'a Joyce Abdulmalik ce ta ba da belin yayin zaman kotun na ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026.
Wane sharadi kotun ta gindaya?
Mai shari'a Joyce Abdulmalik, wadda ita ce ke jagorantar shari’ar, ta umarci waɗanda ake karar da su samar da mutane biyu kowannensu da za su tsaya musu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya musu ya gabatar da takardar mallakar gida na wani babban gida da ke ko dai unguwar Asokoro ko Maitama a Abuja, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Haka kuma, an umarci waɗanda ake karar da su ajiye fasfo dinsu na fita ƙasashen waje a hannun kotu.
DSS na tuhume-tuhume kan Malami
An gurfanar da Malami da ɗansa ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta zargi Malami da kin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci waɗanda aka ce an tura fayil dinsu zuwa ofishinsa domin a yi musu shari’a.
A cewar takardar tuhumar, ana zargin Malami da cewa “yana sane wajen taimaka wa daukar nauyin ta’addanci” ta hanyar kin fara shari’ar mutanen da ake zargi, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 26(2) na dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022.
An samu makamai gidan Malami
Haka kuma, DSS ta yi zargin cewa an samu Malami da ɗansa da mallakar wata bindiga ƙirar Sturm Magnum 17-0101, da harsasai guda 16 na Redstar AAA 5’20, da kuma harsasai guda 27 a gidansu da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi, ba tare da lasisi ba.
Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa mallakar wannan bindiga da harsasai ya kai matsayin shirin aikata ta’addanci, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 29 na dokar hana ta’addanci ta 2022.

Source: Facebook
Malami da dansa dai sun bayyana cewa ba su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Lauyan masu gabatar da ƙara, A.U. Igwe, ya shaida wa kotun cewa an mayar da fayil ɗin shari’ar zuwa sashen gabatar da kara na jama’a (DPP) domin ci gaba da aiki a kai.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Maris 2026.
Alkali ya janye hannunsa a shari'ar Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai shari'a Obiora Egwuatu, ya janye daga jagorantar shari'o'in da suka shafi Abubakar Malami da gwamnatin tarayya.
Kafin janyewarsa, mai shari'a Obiora Egwuatu yana jagorantar shari'o'i biyu da ake yi tsakanin tsohon Ministan shari'ar da hukumar EFCC.
Mai shari'a Egwuatu ya bayyana cewa ya yanke shawarar janye jikinsa ne daga shari'o'in ne saboda dalilai na kashin kansa.
Asali: Legit.ng


