Yadda Kashim Shettima Ya Je Kwara, Ya Ki Ziyartar Kauyukan da Aka Kashe Mutane 200
- Bayan harin 3 ga watan Fubrairu 2026 a Kwara, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura tawaga ta musamman da nufin yin ta’aziyya
- Kashim Shettima wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya bai iya shiga kauyukan Kaiama ba, inda a nan ne aka kashe mutane
- Wasu mutanen yankin Woro sun yi takaicin yadda Mataimakin shugaban kasar ya zo Kwara amma ya yi zamansa a fadar gwamnati a Ilorin
M. Malumfashi ya shafe shekaru kimanin 10 ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kwara - A lokacin da aka kashe mutane da-dama a kauyukan Woro da Nuku, Gwamnatin tarayya ta turo wakilai domin jajanta wa mutanen jihar Kwara.
Sai dai abin da ya yi wa jama’an da ke karamar hukumar Kaiama ciwo shi ne ganin yadda Kashim Shettima da mutanensa suka tare a garin Ilorin.

Source: UGC
Sahara Reporters ta rahoto cewa Sanata Shettima bai iya zuwa kauyukan da nan ne asalin wuraren da aka kai harin ba, sai ya tsaya a babban birni.

Kara karanta wannan
Mun kirga gawawwaki 208 da 'yan ta'adda suka kashe a harin Kwara In ji Mazaunin Woro
Wasu da Legit Hausa ta zanta da su sun nuna yadda wannan abin ya yi masu ciwo a lokacin da aka birne mutane 200 kuma wasu suna can a asibiti.
Kashim Shettima bai ziyarci kauyukan Kaiama ba
A shafin X, Kashim Shettima ya wallafa hotunan lokacin da ya ziyarci Ilorin ba tare da ya karasa Kaiama ba.
“Ba mu san abin da ya sa ya yi haka nan ba, tunda an fada mana cewa yana zuwa.
A lokacin Sanatan Kwara ta Arewa wanda shi ‘dan Kaiama ne, ya iso Ilorin kafin zuwan Mataimakin shugaban kasa da niyyar su dawo nan tare da yiwuwar zuwa Woro…
Muna nan sai aka ji cewa Mataimakin shugaban kasa ba zai zo ranar Alhamis ba sai Juma’a.
A ranar Juma’ar kuma sai mu ka ji an ce (Kashim Shettima) ya tsaya a Ilorin tare da gwamna, shugaban karamar hukumar da sanatanmu.
Wallahi ko Sarkin Woro bai je ba, sai dai shugaban karamar hukuma da Sarkin (Ilorin) suka yi magana.
- Kwamred Muhammad Bashir
A zantawar mu da mutanen yankin, sun nuna ba su ji dadin yadda Mai girma Mataimakin shugaban kasa ya ki zuwa ya ga halin da suke ciki ba.

Source: Twitter
Ya fada mana cewa:
"Gaskiya ba mu ji dadi ba gaskiya, tunda mun fi so ya zo ya ga wajen, ya ga yanayin hanyoyinmu ma. Tsakani da Allah babu wanda ya ji dadin abin nan.
Saboda hanyoyinmu har ka iso cikin Kaiama bai da kyau kuma idan kana shiyyar Neja, haka za ka gani har Woro domin nan ne iyakar karshe da jihar Neja.
Mun tambayi wani malami mazaunin Kaiama game da watsi da su da Shettima ya yi, shi ma ya nuna cewa sam ba su ji dadin wannan lamari ba.
"Gaskiya mutane ba su ji dadi da abin ba, ya zo Kwara amma bai iya zuwa Kaiama inda abin ya faru ba, Wallahi mutane ba su ji dadi ba.
Ka ga shi gwamna ya zo har ya zo wajen kafin zuwan Mataimakin shugaban kasa."
Mene ne abin da mutanen Kaiama suke bukata?
Abin da mutanen yankin suke bukata shi ne samar da cikakken tsaro kuma a share jejin da ke yankin Kainji a Neja domin a tsefe ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
An ji abin da ya roka da Tinubu ya yi waya da Shugaban gwamnatin kasar Jamus a tarho
Matashin ya ce idan an yi haka ne mutane za su dage da yin noma amma muddin aka bar jejin yadda yake, wata rana ‘yan bindiga za su dawo.

Source: Getty Images
Sannan ya roki gwamnatin tarayya ta gyara hanyoyi tun daga Kishi zuwa garin Wawa kuma a tallafa wa mutanen da aka dasa bam aka kona shagunansu.
Shi ma wani ya fada mana dole gwamnati ta yi abin da ya kamata domin hana aukuwar irin wannan abin nan gaba ta hanyar tsefe jejin da ke yankin.
Akwai kasurgumin daji da ke tsakanin iyakokin Kainji da Kaiama inda ake zargin ya fake ‘yan ta’adda.
Sarkin Woro ya koma garin Kaiama bayan harin
Ganin abin da ya faru, Kwamred Bashir Muhammad ya fada mana cewa a lokacin an dauke Sarkin Woro daga kauyen shi, an ajiye shi a cikin garin Kaiama.
Sannan gwamnati ta kafa wani kwamiti mai mutane bakwai da zai duba barnar da aka yi domin ganin matakan da za a dauka na gyara a Woro da Nuku.
Shi sarki yana cikin wannan kwamiti na musamman da aka daura wa nauyi a lokacin da wasu mutanen suke tsere zuwa garuruwan Ilorin, Kainji da Wawa.
Yadda aka kashe mutane a Woro da Nuku
Labari ya gabata cewa wani mutumi ‘dan asalin Woro a Kwara ya shaida mana cewa cikin garin da aka yi jana’iza, mutane 208 suka kirga da aka birne.
Matashin 'dan gwawarmayar ya ce tun kafin karfe 5:00 na yamma ‘yan ta’adda suka kutso cikin kauyukan Woro da Nuku suna kai hari har 2:00 na dare.
Kuma 'yan ta'addan sun sa bam sun yi barna, sun kona shaguna da gidan sarki – sun kashe yaransa biyu kuma sun wuce da matarsa da wata jaririya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng
Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng

