'Yan Kasuwar Man Fetur Na Ci Gaba da Gasar Rage Farashi a Najeriya

'Yan Kasuwar Man Fetur Na Ci Gaba da Gasar Rage Farashi a Najeriya

  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da ganin gasa tsakanin masu kasuwancin man fetur a kasar tun bayan cire tallafin da shugaba Tinubu ya yi
  • Rahoto ya nuna yadda wasu ma’jiyun mai a kasar ke saukewa da tada farashin mai yayin da ake samun ci gaba wajen samu da rashin kaya
  • Babban abin da ‘yan Najeriya suka fi mai da hankali a kansa wajen farashi shi ne man fetur, hakan na daga ginshikin sufuri na kasar

Legas, Najeriya - An fara samawa ‘yan Najeriya sauki bayan da masu ma’ajiyar man fetur masu zaman kansu a fadin ƙasar suka rage farashin fetur, lamarin da ya ƙara tsananta gasa a kasuwar mai ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ragin farashi ya biyo bayan sauye-sauyen da aka samu kwanan nan a farashin fetur a gidajen mai.

Gasa tsakanin manyan masu samar da mai, ciki har da matatar Dangote, na taka muhimmiyar rawa wajen saukar da farashin man.

Kara karanta wannan

An fadi wadanda suka taimaka aka zubar da jinin Musulmai kusan 200 a Kwara

Yadda ake ci gaba da gasar farashin man fetur a Najeriya
'Yan Najeriya za su mori gasar man fetur a kasar | AFP
Source: Getty Images

Sabbin farashi a ma’ajiyun mai

A Legas, wasu manyan ma’ajiyun mai sun sauke farashin fetur zuwa ƙasa da N800 kan kowace lita domin jawo kwastomomi.

  • Aiteo ya saukar da farashi daga N797 zuwa N796.
  • Wosbab da Shellplux sun rage daga N800 zuwa N798.

Wannan ya dan yi ƙasa da farashin abokan hulɗar matatar Dangote wanda ke kusan N799 kan lita, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Haka kuma farashin dizal ya ragu a wasu wurare. Ibeto da Aiteo sun rage daga N917 zuwa N907, yayin da African Terminal ya saukar daga N919 zuwa N909 kan lita.

Halin da ake ciki a wasu jihohi

  • Warri: Wasu ma’ajiyu sun rage farashi (misali Nepal daga N820 zuwa N816), yayin da wasu suka ɗaga saboda ƙarancin mai.
  • Port Harcourt: Farashi na motsi tsakanin N829 zuwa N853, gwargwadon samuwar kaya.
  • Calabar: An samu sauƙi daga kusan N833/N837 zuwa N816, duk da cewa ƙarancin kaya na hana ƙarin sauka sosai.

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun fara cin moriyar dokokin haraji, an fara gani a albashin Janairu

Tasirin gasa a kasuwar mai

Masana na ganin cewa wannan saukar farashi alama ce ta yadda kasuwar man fetur ke ƙara buɗewa, inda masu ma’ajiyar mai masu zaman kansu ke ƙara tasiri kan yadda farashi ke motsi a ƙasa.

Ana sa ran farashin fetur da dizal zai ci gaba da sauyawa gwargwadon sabbin bukatu da tsare-tsaren farashi.

Tun bayan cire tallafin man fetur a Najeriya ‘yan kasar ke fuskantar tsadar mai, lamarin da ke taba dan taro-sis da suke samu na shiga yau da kullum.

Sai dai, gwamnatin kasar na bayyana irin alherin da ta samu na karin kudaden shiga tun bayan cire tallafin a shekarar 2023.

Tasirin matatar Dangote a man Najeriya

Matatar man Dangote ta kasance mai kai komo wajen yawan sauya farashin man fetur a kasar daidai da bukata da samuwar kaya.

Hakazalika, matatar ta samar da gasa tsakanin gwamnati da ma ‘yan kasuwa masu zaman kansu wajen samar da mai a kasar.

Duk da haka, farashin mai a Najeriya bai koma kusa da inda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya same shi ba a lokacin da ya karbi mulki a watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng