Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Wani Babban Jigo a Jam'iyyar APC
- Shugaban Karamar Hukumar Ilaje a Ondo, Maurice Oripenaye, ya bayyana damuwa bayan sace wani jigo na APC
- Oripenaye ya ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki ofishin Emorioloye inda suka tafi da shi a cikin motoci Hilux biyu
- ‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa bincike ya fara, tare da kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ondo - Shugaban Karamar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo, Mista Maurice Oripenaye ya koka kan harin yan bindiga .
Oripenaye ya bayyana damuwa kan sace wani jigo na jam’iyyar APC, Mista Owoloemi Emorioloye.

Source: Twitter
Yan bindiga sun sace jigon APC
A cikin wata sanarwa da ya fitar, wanda Vanguard ta samu, Oripenaye ya ce wasu mutane dauke da makamai sun sace Emorioloye ne a ofishinsa.
Ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis, inda ‘yan bindigar suka zo da motoci Hilux guda biyu, suka kai farmaki cikin tsakar rana.
Shugaban karamar hukumar ya ce tun bayan faruwar lamarin, ba a san inda Emorioloye yake ba, duk da kokarin tuntubarsa.
Oripenaye ya yi Allah-wadai da wannan danyen aiki, yana mai kiran jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da ceto wanda aka sace lafiya.
A cewarsa, sace Emorioloye barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar al’ummar Ilaje, musamman ganin cewa lamarin ya faru a fili.
Ya bayyana cewa shaidun gani da ido sun nuna yadda ‘yan bindigar suka dauke Emorioloye da karfi daga ofishinsa a yankin.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci jama’a da su guji yada jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, don kada a tayar da hankula.
Ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin mazauna Ilaje shi ne babban abin da ya sa a gaba a matsayinsa na shugaban karamar hukuma.
Oripenaye ya ce an riga an tuntubi jami’an tsaro daban-daban, ciki har da ‘yan sanda, DSS, sojoji da kungiyoyin tsaro na gargajiya.

Source: Original
Martanin 'yan sanda kan harin Ondo
A nasa bangaren, kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar sacewar Emorioloye, cewar Punch.
Jimoh ya ce rundunar ta fara cikakken bincike, tare da daukar matakan tsaro domin tabbatar da lafiyar rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Ya bukaci al’ummar Ondo da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar na aiki tukuru domin gano gaskiyar lamarin.
‘Yan sanda sun ce dukkanin bayanan da ke hannunsu a yanzu kadan ne, amma bincike mai zurfi yana gudana kan lamarin.
Yan bindiga sun sace dan India a Oyo
Kun ji cewa mutane sun shiga tashin hankali da yan bindiga suka kai hari a cikin gona inda suka hallaka jami'in dan sanda da ke gadinta.
An kai harin ne a gonar Aqua Triton a Ogunmakin, Ibadan da ke jihar Oyo inda suka sace wani ɗan ƙasar waje.
Marigayi dan sandan mai suna Imoobe Prester, ya yi artabu da ’yan bindigar domin hana satar, amma aka harbe shi har lahira.
Asali: Legit.ng

