Sheikh Gumi Ya Aika Sako ga Tinubu bayan Harin Amurka a Sakkwato

Sheikh Gumi Ya Aika Sako ga Tinubu bayan Harin Amurka a Sakkwato

  • Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da duk wani haɗin gwiwar soji da Amurka nan take
  • Malamin ya yi gargaɗin cewa tsoma bakin Amurka na iya maida Najeriya filin yaƙi musamman bayan harin da ta kai wani kauye da ke jihar Sakkwato
  • Sheikh Gumi ya ba da shawarar a nemi taimakon soji daga ƙasashe masu “tsaka-tsaki” kamar China, Turkiyya da Pakistan domin magance matsalolin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Shehin malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta katse duk wata hulɗar soji da Amurka.

Sheikh Gumi ya kara da bayyana cewa ci gaba da haɗin gwiwa da Amurka zai iya jefa ƙasar cikin mummunan yanayin tsaro tare da maida ta “filin wasan yaƙi”.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Najeriya ta ce game da harin Amurka a Sakkwato

Sheikh Gumi ya gargadi gwamnatin Najeriya
Donald Trump na Amurka, Sheikh Ahmad Gumi, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Donald J Trump/Dr. Ahmad Mahmoud Gumi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: UGC

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gumi ya bayyana hakan ne bayan rahoton hare-haren sama da Amurka ta kai kan mayaƙan ISIS a ranar Kirsimeti.

Sheikh Ahmed Gumi ya caccaki Amurka

Dr. Ahmad Gumi ta bayyana cewa tsoma bakin ƙasashen waje, musamman Amurka, ba zai kawo ƙarshen matsalar tsaro ba, sai dai ƙara rura wutar rikici.

Malamin addinin ya ce ya kamata Najeriya ta nemi tallafin tsaro daga ƙasashe da ya bayyana a matsayin masu tsaka-tsaki, ciki har da China, Turkiyya da Pakistan.

Ya ce:

“Shigar Amurka cikin harkokin tsaron Najeriya zai jawo ainihin maƙiyan Amurka, wanda hakan zai sa ƙasarmu ta koma filin yaƙi. A ƙa’ida, babu wata ƙasa da ya kamata ta amince a mayar da ƙasarta filin yaƙi, ko kuma ta bari maƙwabtanta su zama maƙiyanta.”

Duk da amincewa da halaccin yaƙi da ta’addanci, Gumi ya jaddada cewa bai kamata a miƙa wannan nauyi ga ƙasashen waje ba, yana zargin cewa galibinsu na da wata manufa ta ɓoye.

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun kawo hari Najeriya don 'kare rayukan kiristoci '

Ya ce:

“Kashe ‘yan ta’adda wajibi ne a Musulunci, kamar yadda Hadisin Annabi Muhammad (SAW) ya nuna. Amma dole ne a yi hakan da hannaye masu tsarki, ba hannun wasu ‘yan ta’adda da jinin fararen hula—mata, yara da maza—ya cika hannuwansu ba.”

Gumi ya shawarci gwamnatin Najeriya

Sheikh Gumi ya kuma bayyana cewa dogaro da Amurka wajen yaƙi da ta’addanci kuskure ne, yana mai cewa “’yan ta’adda ba sa yaƙar ‘yan ta’adda da gaske.

A kalamansa:

"Sau da yawa fararen hula ne ke shan wahala, tare da wata manufa ta ɓoye a bayan kiran yaƙin ‘ta’addanci’.”

Ya yi gargaɗin cewa tsoma bakin Amurka, musamman da hujjar kare Kiristoci, na iya ƙara rarrabuwar addini tare da tauye ikon Najeriya.

Sheikh Gumi ya ce akwai illa a alaka da Amurka
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Gumi ya ce:

“Shigowar Amurka da hujjar kare Kiristoci zai iya raba kan ‘yan Najeriya tare da take ikon ƙasarmu."

Malamin ya ƙara da cewa batun tsaro zai kasance muhimmin jigo a siyasar 2027, yana mai cewa ‘yan Najeriya sun waye, ba za a ruɗe su ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya maka wasu mutum 2 a kotu kan rubutun da suka yi a Facebook

Ya kuma jaddada cewa hare-haren sama kaɗai ba za su kawar da ta’addanci ba, yana kiran a tura sojoji ƙasa tare da amfani da ƙarfin da Najeriya ke da shi.

Amurka ta kawo hari Najeriya

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kaddamar da hare-haren sama kan wasu wurare da ake zargin ‘yan ta’addar ISIS ke fakewa a Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihar Sakkwato.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce shi da kansa ya bayar da umarnin kai harin, inda ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na dakile hare-haren ‘yan ta’adda da kuma kare rayukan Kiristoci.

Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afrika, AFRICOM, ta tabbatar da cewa an kai hare-haren ne bisa buƙatar hukumomin Najeriya, tare da hadin gwiwa da jami’an tsaron kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng

Tags: