Gwamna Fubara Ya Fadi Biliyoyin da Ya Tarar a Asusun Rivers bayan Soke Dokar Ta Baci
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana kudin da ya bari a asusun gwamnati kafin sanya dokar ta baci
- Mista Siminalayi Fubara ya bayyana dukkan bayanai kan kudin da ya kashe suna nan kuma jama'a za su iya ganin su
- Hakazalika, gwamnan ya fadi kudin da ya tarar a lalitar jihar bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta baci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan kudin da ya tarar a asusun gwamnati bayan dawowa kan mulki.
Gwamna Simi Fubara ya bayyana cewa ya tarar da fiye da Naira biliyan 600 a asusun jihar lokacin da aka cire dokar ta-ɓaci.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Fubara ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025, yayin kaddamar da titin Obodhi–Ozochi mai tsawon kilomita 14.2.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da jajircewa wajen tafiyar da kuɗaɗen jama’a cikin tsari da gaskiya.
Gwamnan ya bayyana cewa ya bar kimanin Naira biliyan 300 a asusun gwamnati kafin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da hakan.
An soki Gwamnan Rivers, Simi Fubara
Jawabinsa ya zo ne a daidai lokacin da shugaban majalisar dokokin jihar Rivers, Rt. Hon. Martin Amaewhule, ke sukar halin da makarantun gwamnati ke ciki.
Shugaban majalisar dokokin ya kuma yi tambayoyi kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da tsohon shugaban riko na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya bari.
Amaewhule ya bayyana a wani zama na majalisa kwanan nan cewa Ibas ya mika fiye da Naira biliyan 600 bayan an janye dokar ta-ɓaci.
Wane martani Gwamna Fubara ya yi?
Da yake mayar da martani, Gwamna Fubara ya ce ana amfani da dukkan kuɗaɗen jihar cikin gaskiya, tare da bayyana cewa bayanan kashe-kashe na gwamnatinsa a bayyane suke kuma ana iya tantance su.
“Yau ina so na faɗa wa duniya baki ɗaya. Lokacin da muka bar ofis saboda dokar ta-ɓaci, duk bayananmu suna nan. Mun bar sama da Naira biliyan 300. Da muka dawo, mun tarar da kusan Naira biliyan 600 da wani abu a kai."
"Idan akwai abin da zan ce ina alfahari da shi, babu wanda zai danganta ni da wani abin rashin gaskiya. Don haka kuɗaɗenku da kuma bayanan yadda ake kashe su suna nan lafiya. Muna aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri”
- Gwamna Siminalayi Fubara

Source: Twitter
Gwamnan Rivers zai fitar da bayanai
Gwamna Fubara ya ba wa al’ummar jihar tabbacin cewa cikin watanni shida, gwamnatinsa za ta gabatar da cikakkun bayanai masu bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen jama’a.
Ya danganta wasu daga cikin sukar da ake yi wa gwamnatinsa da tsarin da ya ɗauka na kammala ayyuka gaba ɗaya kafin kaddamar da su, maimakon yin shagulgulan fara aiki kawai.
“Wataƙila dalilin da ya sa wasu ke tunanin akwai abin da ke faruwa da ba su sani ba, shi ne ba mu yarda da kaddamar da aikin da bai kammala ba. Mu mun yarda da kaddamar da aikin da aka gama."

Kara karanta wannan
Gwamna Diri ya umarci gudanar da bincike bayan mataimakinsa ya yi mutuwar farat daya
- Gwamna Siminalayi Fubara
Gwamna Fubara ya magantu kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi tsokaci kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Gwamna Fubara wanda ya sauya sheka zuwa APC mai mulki ya sake jaddada cewa a shirye yake ya goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Hakazalika, gwamnan ya kuma bukaci mutanen jihar Rivers da su ci gaba da nuna goyon baya ga Mai girma Bola Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

