Gwamna Diri Ya Umarci Gudanar da Bincike bayan Mataimakinsa Ya Yi Mutuwar Farat Daya
- Ana ci gaba da jimamin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo wanda ya yi bankwana da duniya
- Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya nuna damuwa kan maganganun da ake yi dangane da rasuwar mataimakin nasa
- Douye Diri ya bayyana cewa ya ba da umarnin a gudanar da bincike domin gano musabbabin dalilin rasuwar Lawrence Ewhrudjakpo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi jimamin rasuwar mataimakinsa.
Gwamna Diri ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gawa, domin gano musabbabin mutuwar mataimakin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 13 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Diri ya karbi bakuncin Jonathan
Gwamna Diri ya yi magana ne yayin da yake karɓar bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a gidan gwamnatin jihar Bayelsa da ke Yenagoa.
Lawrence Ewhrudjakpo ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya faɗi a ofishinsa. An garzaya da shi zuwa asibitin FMC Yenagoa, inda aka tabbatar da rasuwarsa bayan sun isa asibitin.
Diri ya umarci a yi bincike
Gwamna Diri ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “yawan shirme da ake yadawa a kafafen sada zumunta” game da mutuwar Ewhrudjakpo, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a siyasantar da rasuwarsa ba, jaridar Daily Trust ta dauko labarin.
“Ina so na yi kira. Na ga mutane suna siyasantar da mutuwarsa. A kasar Ijaw, babu gaba a cikin mutuwa. Kada wani ya siyasantar da mutuwar mataimakin gwamnanmu. Duk wanda yake kaunarsa, wannan ne lokacin da zai nuna hakan.”
“Na bayar da umarnin a yi binciken gawarsa domin gano musabbabin mutuwarsa. Akwai yawan shirme da ake yi a kafafen sada zumunta.”
“Idan wani yana fitar da sanarwa domin yi masa ta'aziyya, to a tsaya a nan kawai, a yi masa makoki, domin jihar na cikin yanayin jimami."
"Shi ya sa muka ayyana ranaku uku na zaman makoki, kuma muna sa ran kowa a jihar ya yi abin da tsohon shugaban kasa ya yi a yau.”
“Mu kaunaci juna har zuwa mutuwa, domin dukkanmu wata rana za mu amsa wannan kiran.”
- Gwamna Douye Diri

Source: Twitter
Me Jonathan ya ce kan Lawrence?
Da yake jawabi yayin ziyarar, Goodluck Jonathan ya bayyana marigayi Ewhrudjakpo a matsayin mutum da ba zai taɓa mantawa da shi ba.
Tsohon shugaban kasar ya ce Ewhrudjakpo ya yi aiki tukuru a matsayin mataimakin gwamna fiye da yadda shi kansa ya yi a lokacin da yake rike da wannan muƙami.
“A gare ni, mutum ne mai matukar muhimmanci ga gidauniyata, kuma ba zan taɓa mantawa da shi ba. Shi ne yake wakiltar gwamna a dukkan shirye-shiryenmu.”
- Goodluck Jonathan
Diri ya kadu da rasuwar mataimakinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi alhini kan rasuwar mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.
Gwamna Douye Diri ya ce mutuwar marigayin ta girgiza shi matuƙa, tare da barin gibi mai girma a harkokin mulki da rayuwar al’ummar jihar.
Ya ce dangantakarsu ba ta ta’allaka ne a kan ubangida da mataimaki ba, illa ta kasance ta ’yan’uwa da abokai masu girmama juna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

