Yadda Gobara ta Lakume Sashen Kayat Restaurant a Birnin Maiduguri
- Gobara ta tashi a Kayat Restaurant da ke Polo Road a birnin Maiduguri, inda ta ƙone manyan sassn ginin gidan cin abincin
- Jami’an kashe gobara da ’yan sanda sun yi gaggawar kawo ɗauki, inda suka takaita yaduwar wutar cikin kankanin lokaci
- Har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba yayin da ake ci gaba da bincike da duba asarar da aka tafka a ginin
Maiduguri, Borno – Gobara mai ƙarfi ta tashi ranar Lahadi a gidan cin abincin Kayat Restaurant da ke Polo Road a birnin Maiduguri, lamarin da ya shafi babban ɓangare na ginin.
Wutar, wadda ta fara misalin ƙarfe 11 na safe, ta ja hankalin mazauna yankin kafin jami’an kwana-kwana na jihar Borno da ’yan sanda su kawo ɗauki cikin gaggawa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto da kashe wutar.

Source: Twitter
A kalamansa:
“Tawagar mu daga ofishin ’yan sanda na GRA na nan suna taimaka wa jami’an kashe gobara.”
Shaidu sun bada bayanai kan yadda gobarar ta auku
Wani shaidan gani da ido mai suna Umar Abdullahi ya bayyana cewa an kebe yankin gaba ɗaya domin kiyaye jama’a.
Ya ce:
“Na wuce can yanzu haka. Wani babban ɓangare na wurin har yanzu na ci gaba da ci da wuta. Amma akwai jami’an kashe gobara suna ƙoƙarin kashe ta.”
Wata majiya, Martina Joseph, ta ce an yi aikin ceton cikin kwarewa, inda aka killace mutane da motocin da ke kusa da wurin domin kauce wa cunkoso da yaduwar wuta.
Ta ce:
“Sun gudanar da kome cikin tsari. Sun takaita motsin jama’a da motoci da sauri. Abin da na gani shi ne ginin da wasu kayayyaki ne suka kama da wuta.”
Babu tabbacin abin da ya haddasa gobarar
Har yanzu ba a gano dalilin da ya haifar da gobarar ba. An yi ƙoƙarin tuntubar Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar kashe gobara ta kasa a Borno, Fati Fali Murtala, amma hakan bai yi nasara ba a lokacin da ake tattara rahoton nan.
A watan Maris, jaridar Punch ta ruwaito irin wannan gobara da ta ƙone shagunan na’urorin lantarki a Monday Market a birnin na Maiduguri, lamarin da ya jawo asara mai yawa.
A lokacin, rundunar ’yan sandan Borno ta tura jami’ai domin tsare wurin da kuma hana sata yayin aikin ceto.
Ana yawan samun gobara da tashin wuta a yankuna daban-daban na Najeriya, lamarin da ke jawo asarar dukiya da rayuka a wasu lokutan.
Gobara a kasuwar Singa a Kano
A wani labarin, wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta kona shaguna 25 a kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano.
Jami'an hukumar kashe gobara sun ce wutar ta haifar da babbar asara ta dukiya kafin a shawo kanta.
Leadership ta ce hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Talata.
Asali: Legit.ng

