Gwamna Okpebholo Ya Koka kan Basussukan da Ya Gada wajen Magabacinsa
- Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi bikin cika shekara daya a kan madafun ikon jihar da ke yankin Kudu maso Kudu
- Monday Okpebholo ya bayyana cewa ya samu jihar cikin wani mawuyacin hali lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2024
- Hakazalika, Gwamna Okpebholo ya bayyana irin dumbin basussukan da aka tafi aka bar shi da biya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi magana kan yadda ya tarar da jihar bayan ya hau kan karagar mulki.
Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa lokacin da ya karɓi mulki, ya tarar da jihar tana cikin mawuyacin hali na bashi, rashin tsaro, da lalacewar abubuwa a fannoni da dama.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, Gwamna Okpebholo ya bayyana haka ne a birnin Benin a ranar Laraba yayin bikin cikar shekararsa daya a kan mulki.

Kara karanta wannan
Bayan komawa APC, Gwamna Diri ya magantu kan tilastawa mataimaminsa dawowa jam'iyyar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da Okpebholo ya tarar da Edo
Gwamna Okpebholo ya ce tun bayan hawansa, ya fara dawo da martabar gwamnati da samar da amincewar jama’a ta hanyar karfafa hukumomi da tsare-tsaren mulki.
“Na tarar da jihar cike da tabarbarewa a sassa daban-daban, daga bashi na cikin gida da na waje, rashin tsaro da rashin amincewa."
"Amma na fara dawo da amincewar jama’a ta hanyar gyara hukumomi da inganta shugabanci."
- Gwamna Monday Okpebholo
Gwamnan ya bayyana cewa ya gaji bashin Naira biliyan 600 na cikin gida da na waje, da kuma bashin kwangiloli na Naira biliyan 180 da gwamnatin da ta gabata ba ta biya ‘yan kwangila ba.
Ya ce cikin shekara guda, gwamnatinsa ta rage bashin da ta gada ta hanyar kyakkyawan tsarin kudi, rahoton The Punch ya tabbatar da labarin.
“A cikin shekara guda, mun samar da ayyukan yi kai tsaye da wadanda ba kai tsaye ba fiye da 10,000, sannan mun kaddamar da shirin bada rancen Naira biliyan 1 mara ruwa ga ‘yan kasuwa, masu kanana da matsakaitan sana’o’i.”
- Gwamna Monday Okpebholo
Gwamna Okpebholo ya ce ya kuma gaji hanyoyi da dama da suka lalace da al’ummomi da aka manta da su.

Source: Twitter
Ayyukan da Okpebholo ke yi a Edo
Ya bayyana cewa yanzu gwamnatinsa ta bayar da kwangilar gina sababbin hanyoyi 28 masu tsawon kilomita 350, tare da gine-ginen gadoji biyu a Rama Park da kwanar hanyar Adesuwa a titin Sapele.
Ya kara da cewa lokacin da ya karɓi mulki, jihar Edo ta kusa zama “filin yaki” saboda yawaitar kisan 'yan kungiyar asiri, satar mutane, da fashi da makami.
“Mun dauki matakin gaggawa ta hanyar soke dokar yaki da kungiyoyon asiri mai rauni, mun kafa sabuwar doka mai karfi, mun ba jami’an tsaro motoci 60 na Hilux da babura 400, sannan mun dauki sababbin jami’ai 2,500 a rundunar tsaro jihar Edo."
- Gwamna Monday Okpebholo
Gwamna Okpebholo ya kori kwamishina
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya kori daya daga cikin kwamishinoninsa.
Gwamna Okpebholo Monday Okpebholo, ya sauke Hon. Samson Osagie daga mukaminsa na kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Edo.
Hakazalika, Gwamna Okpebholo ya ƙara adadin ma’aikatun gwamnatin Edo zuwa guda 28, a wani yunƙuri na ƙara daidaito da inganci a gudanar da mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

