Sakin Nnamdi Kanu: Sowore, 'Yan Zanga Zanga Sun Ruga da Gudu bayan Fara Harbi

Sakin Nnamdi Kanu: Sowore, 'Yan Zanga Zanga Sun Ruga da Gudu bayan Fara Harbi

  • Rundunar ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu da harsasai
  • Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ne ya jagoranci masu zanga-zangar a wasu sassa na birnin tarayya Abuja
  • Jami’an tsaro daga ‘yan sanda, DSS, NSCDC da sojojin fadar shugaban kasa sun tsaurara tsaro a manyan wurare a birnin Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu rudani a Abuja yayin da jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar IPOB da ake tsare da shi, Nnamdi Kanu.

Masu zanga-zangar sun ruga da gudu bayan jami’an tsaro sun bude wuta da harsasai domin tarwatsa taron.

Sowore yayin zanga zanga
Sowore yana jagorantar zanga zanga a Najeriya. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa zanga-zangar da Omoyele Sowore ya jagoranta ta gudana ne da sanyin safiya a kusa da hedkwatar ma’aikatar harkokin mata a babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda, Hukumar DSS da NSCDC ne suka tsaurara tsaro a yankin tun ranar Lahadi.

Yadda aka fita zanga zangar Nnamdi Kanu

Kafin jami’an tsaro su fara bude wuta, masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa kusa da kotun daukaka kara inda suka rika rera wakoki da kira da a saki Nnamdi Kanu.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa zanga-zangar nasu ta lumana ce, amma sun yi mamakin yadda jami’an tsaro suka fara kai musu farmaki.

Punch ta wallafa cewa masu zanga-zangar sun fara ja da baya bayan sun ji karar harsasai daga bangarori daban-daban.

Wasu daga cikin su sun bayyana cewa a farkon lokacin sun dauka barkonon tsohuwa ne za a yi amfani da shi, amma sai suka fahimci harsasai ake harbawa.

Maganar Sowore kafin ya ruga da gudu

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya yi kira ga jami’an tsaro da su mutunta ‘yancin jama’a na yin zanga-zanga cikin lumana.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar juyin mulki, an gargadi masu zanga zanga kusantar fadar Tinubu

Ya ce:

“Kada ku yi amfani da barkonon tsohuwa ko harsasai a kanmu! Ku mutunta doka! Muna da ‘yancin yin zanga-zanga — mu ‘yan Najeriya ne.”

Masu zanga-zangar sun ce manufarsu ita ce jan hankalin gwamnati kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu duk da umarnin kotu da ke bukatar a sake shi.

Sowore ya ruga da gudu
Sowore yana gudu daga filin zanga zanga a Abuja. Hoto: Hassan Dan Maliki
Source: Facebook

Kafin su ruga da gudu, sun bayyana wa jami'an tsaro cewa ba su da niyyar tada tarzoma ko yin barna.

Halin da ake ciki bayan zanga-zanga

Bayan tarwatsa zanga-zangar, an ci gaba da ganin motocin yaƙi da na sulke daga rundunar Guards Brigade da ‘yan sanda suna sintiri a yankin.

Rahotanni sun ce an kafa shingaye a hanyoyin da ke kaiwa fadar shugaban ƙasa, Majalisar Dokoki ta Kasa, Kotun Daukaka Kara da kuma Eagle Square.

A halin yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan harbe-harben ba, sai dai ganau sun ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun samu raunuka yayin gudu daga wurin.

Kara karanta wannan

MCAN: 'Yan NYSC Musulmi sun yi taron Arewa maso Gabas a Gombe

Ana bincike kan juyin mulki a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wasu bayanai sun nuna cewa ana cigaba da bincike kan zargin juyin mulki da aka ce an shirya a Najeriya.

Wata majiya ta ce hukumomi sun saka ido a kan wani tsohon gwamna daga Kudancin Najeriya kan zargin yana da hannu a lamarin.

Bayan saka ido da ake a kan tsohon gwamnan, rahotanni sun ce za a gayyace shi ya amsa tambayoyi idan aka samu yana da alaka da yunkurin juyin mulkin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng