Matasan Jihar Kaduna Sun Nuna Bajinta, An Samu Miliyoyi a NBC 2025

Matasan Jihar Kaduna Sun Nuna Bajinta, An Samu Miliyoyi a NBC 2025

  • An kammala wani taro na musamman da kamfanin BTC ya shirya domin inganta rayuwar matasa a jihohin Najeriya
  • Jihar Kaduna ta yi abin a yaba a shekarar bana domin matasanta ne aka samu sun zo na farko, sun sha gaban sauran jihohi
  • Wadanda suka yi nasara sun samu kyautar kudi da za su yi amfani da shi a matsayin jari domin su bunkasa kasuwancinsu

Editan Legit Hausa Muhammad Malumfashi yana da ƙwarewar shekaru kusan 10 wajen kawo rahotannin siyasa, addini da wasanni.

Kaduna - A watan Satumba ne kamfanin BTC ya shirya wani gangamin yawon shakatawa na musamman da aka warewa matasa.

A taron na wannan shekarar da aka yi, matasan da suka fito daga jihar Kaduna sun ciri tura kamar yadda bayanai suka tabbatar.

NBS/BTC
Wasu matasa daga jihohi a taron BTC Hoto: Legit
Source: Original

'Yan Kaduna sun yi fice a NBC 2025

Legit Hausa ta samu labari cewa matasan Kaduna sun ciri tuta a shirye-shiryen da aka tsara domin bunkasa rayuwar manyan goben.

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tsawon kwanakin da aka yi ana wannan taro, matasa sun karu da ilmomi iri-iri kuma an kara masu kwaurin guiwar ayyukan da suka sa a gaba.

Mun fahimci cewa wadanda aka yi taron da su sun samu karin haske a kan sha’anin kasuwanci, wannan zai ba su damar juya taro da sisi.

Har ila yau, a wannan zama da aka yi, an koyar da matasan game da hulda da abokan cinikiyya, hanyoyi sadarwa, kula da ayyuka da tsara kasuwanci.

NBC 2025
Wasu matasa wajen shirin NBC Hoto: Legit
Source: Original

Kwararrun mutane sun koyawa matasan yadda za su cin ma burin rayuwarsu ta hanyar kawo misali da wasu abubuwa na rayuwa.

Da dama daga cikin matasan sun kuma samun jarin kasuwanci wanda hakan zai taimaka masu wajen harkokin neman kudi a Kaduna.

Daga lokacin da aka fito da shirin a 2017 zuwa yanzu, matasa fiye da miliyan daya sun amfana, wanda ake sa ran hakan zai rage talauci.

Jaridar Business Day ta rahoto cewa a ranar 26 ga watan Satumba aka bude shirin wannan shekarar tattare da matasa daga jihohi.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun yi wa matar sarki tsirara, an lakadawa sarki da yarima duka

Matasa sun samu N1m a NBC 2025

A taron bana an zabi mutane uku da kowane zai samu N1m domin habaka kasuwancin da yake yi a irinsu harkokin abinci da makamantansu.

Ganin gagarumar nasarar da aka samu a shekarar nan ta 2025, a nan gaba kuma kamfanin zai shiga jihohin Benuwai, Ondo, Fatakwal.

Sauran jihohin da za a leka wannan karo sun hada da Edo, Neja, Jos da kuma Delta daga Kudu da kuma Arewacin kasar nan.

A 2024 da aka yi irin wannan taro, dubban matasa daga jihohin Abuja, Ogun, Oyo, Enugu, Lagos, sai kuma Kano, Anambra da Borno.

SERAP za ta iya yin karar jihohi a kotu

A baya an ji labari kungiyar SERAP ta bukaci dukkan gwamnonin Najeriya da ministan Abuja su bayyana yadda suka kashe kudinsu.

SERAP ta ce gwamnoni da ministan Abuja sun samu kusan Naira tiriliyan 14 bayan cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi a Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Zuwa kotu da abubuwan da ake fada kan takarar Jonathan a 2027

Kungiyar ta yi ikirarin cewa duk da kudin da suka samu ba a ga wasu abubuwan cigaba a kasa ba a cikin wadannan watanni a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng