Fusatattun Matasa Sun Kona Gidan Basarake a Binuwai, Sun Bayyana Dalilinsu
- Matasa a Jihar Binuwai sun bayyana fushinsu a kan zargin wani jami'in soja da harbe daya daga cikinsu har lahira ba tare da dalili ba
- Rikicin ya samo asali ne daga wani harin da ake zargin sojojin Najeriya suka kai a Jato Aka yayin dawowar mutane daga jana’iza
- Har zuwa lokacin wallafa labarin, gwamnatin Jihar Binuwai ba ta fitar da wata sanarwa ba game da lamarin ba yayin da matasa su ka yi kone-kone
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue – Yayin da 'yan Najeriya ke murnar Ranar 'Yancin Kai a jiya, wani mummunan lamari ya faru a yankin Jato Aka na karamar hukumar Kwande a Jihar Binuwa.
Daruruwan matasa a garin sun fito zanga-zangar adawa da kisan gilla da su ke zargin sojojin Najeriya na yi ba tare da an hukunta su ba.

Kara karanta wannan
An hallaka shedanin dan bindiga, matasa sun kona fadar Sarki da harsashi ya samu dalibai

Source: Twitter
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa wani ganau, Iorkohol Asemave, ya shaida mata cewa sojojin Najeriya da ke aiki a Jato Aka sun harbi wasu mutane a garin.
Ana zargin sojoji da harbi a Binuwai
Wanda lamarin ya faru a kan idonsa, Iorkohol Ademave ya ce sojoji sun bude wa jama'a wuta a hanyar dawowa daga jana'izar Cif Hanave Laha, wanda shi ne shugaban al’ummar Nzaav.
A cewarsa, an kashe wani mutum da aka bayyana sunansa da Mr Iorsuur nan take, yayin da aka jikkata wani dalibi na makarantar sakandiren kimiyya ta gwamnati, Jato Aka.
Shaidu sun kara da cewa sojojin sun dauki gawar marigayi Iorsuur daga wurin da abin ya faru zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.
Matasan Binuwai sun fusata
Bayan faruwar lamarin, matasa cikin fushi suka kona gidan Mai Martaba Simon Baver, sarkin Turan, wanda ke kusa da inda lamarin ya faru.
Matasan sun dauki hakan a matsayin martani ga hukuma mafi kusa da su domin bayyana takaicin abin da ya faru kuma babu wani bayani da ya biyo baya.
Duk da zafin da al'amarin ya dauka, Kyaftin Abdullahi Lawal Osabo, mai magana da yawun sojojin musamman, ya ki cewa komai a kan fauwar lamarin saboda yana hutu.

Source: Original
A halin yanzu, an tsaurara matakan tsaro a Jato Aka inda sojoji ke sintiri cikin manyan motoci dauke da makamai. Kasuwanci da harkokin yau da kullum sun tsaya cak.
Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, gwamnatin Jihar Binuwai ba ta fitar da wata sanarwa ba game da rikicin.
Sojoji sun hallaka 'dan bindiga a Binuwai
A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar Operation Whirl Stroke ta kashe wani shahararren ɗan bindiga yayin musayar wuta da aka yi a Jato‑Aka, a jihar Binuwai.
Lamarin ya faru ne lokacin da sojojin ke sintiri a yankin, suka hango wani rukuni da ake zargin yan bindiga ne a kan babura da makamai, sannan aka bude wuta.
Duk da cewa harbi aka yi domin mayar da martani ga masu laifi, harbin ya rutsa da wasu marasa laifi: ɗalibai uku ne suka samu raunuka; daga cikinsu, mace ta rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
